Surah Al-Baqarah | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 10
Suratul Al-Baqarah from 62 to 69
62. Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, da waɗanda suka tũba ( 1 ) , da Nasãra da Makarkata, wana ya yi ĩmani da Allah da Yinin Lãhira, kuma ya aikata aikin ƙwarai, to, suna da ijãrarsu a wurin Ubangijinsu, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba.
63. Kuma a lõkacin da Muka riƙi alƙawarinku, kuma Muka ɗaukaka dũtse a bisa gareku: « Ku kãma abin da Muka baku da ƙarfi. Kuma ku ambaci abin da yake a cikin sa, tsammãninku ku kãrekanku. »
64. Sa'an nan kuma kuka jũya daga bayan wancan, to, bã dõmin falalar Allah ba da rahamarSa a kanku, haƙĩƙa, dã kun kasance daga mãsu hasãra. « »
65. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, kun san waɗanda suka ƙẽtare haddi daga gare ku a cikin Asabar, sai muka ce musu: « ku kasance birai ƙasƙantattu. »
66. Muka sanya ta ( mas'alar ) azãba, dõmin abin da yake gaba gareta, da yake a bãyanta, kuma wa'azi ga mãsu taƙawa.
67. Kuma a lõkacin da Musa yace ga mutanensa: « Lalle ne, Allah Yana umurtar ku da ku yanka wata sãniya. » Suka ce: « Shin kana riƙon mu ne da izgili? » Ya ce: « Ina nẽman tsari daga Allah da in kasance daga jãhilai. »
68. Suka ce: « Ka rõƙa mana Ubangijinka, Ya bayyana mana, mecẽ ce ita? » Ya ce: « Lalle ne, Shi, Yana cewa: » Lalle ne ita sãniya ce; bã tsõfuwa ba, bã kuma budurwa ba, tsakãtsaki ce a tsakãnin wancan,' sai ku aikata abin da ake umurninku. « »
69. Suka ce: « Ka rõƙa mana Ubangijinka Ya bayyana mana abin da yake launinta. » Ya ce: « Lalle ne, Shi Yana cewa: » Ita wata saniya ce fatsa- fatsa, mai tsan- tsan launi, tana faranta ran mausu kallonta. « »
( 1 ) Waɗanda suka koma, watau Yahũdu, daga maganar Mũsa, « Mun kõma garesu » Sura ta 7 aya ta 156, kuma Makarkata, jama'a ce daga Lãrabãwa suka karkata daga addĩnin ubanninsu zuwa ga bauta wa malã'iku. A farkon Musuluncisunã cẽwa ga wanda ya musulunta, wai ya yi kama da su.