Hausa translation of the meaning Page No 116

Quran in Hausa Language - Page no 116 116

Suratul Al-Ma'idah from 46 to 50


46. Kuma Muka biyar a kan gurãbansu da Ĩsa ɗan Maryama, yãnã mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Attaura, kuma Muka bã shi Injĩla a cikinsa akwai shiriya da haske, yanã mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Attaura, kuma shi shiriya ne da wa'azi ga mãsu taƙawa.
47. Kuma sai mutãnen injĩla su yi hukunci da abin da Allah ya saukar a cikinta. Kuma wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah ya saukar, to, waɗannan su ne fãsiƙai.
48. Kuma Mun saukar da Littãfi zuwa gare ka da gaskiya, yanã mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Littãfi ( Attaura da Injĩla ) , kuma mai halartãwa a kansa. sai ka yi hukunci a tsakãninsu da abin da Allah Ya saukar kuma kada ka bĩbiyi son zũciyõyiniu daga abin da ya zo maka daga gaskiya ( 1 ) . Ga kõwanne daga gare ku Mun sanya sharĩa da hanya ( ta bin ta ) . Kuma dã Allah Yã so, dã Yã sanya ku al'umma guda, kuma amma dõmin Ya jarraba ku a cikin abin da Ya bã ku. Sai ku yi tsere ga ayyukan alheri. Zuwa ga Allah makõmarku take gabã ɗaya. Sa'an nan Ya bã ku lãbãri ga abin da kuka kasance kunã sãɓãwa a cikinsa.
49. Kuma ka yi hukunci a tsakãninsu da abin da Allah Ya saukar kuma kada ka bĩbiyi son zũciyõyinsu, kuma ka yi saunar su fitine ka daga sãshen abin da Allah Ya saukar zuwa gare ka. To, idan sun juya bãya, to, ka sani cewa, kawai Allah yana nufin Ya sãme su da masĩfa ne sabõda sãshen zunubansu. Kuma lalle ne, mãsu yawa daga mutãne, haƙĩƙa, fãsiƙai ne.
50. Shin, hukuncin Jãhiliyya ( 2 ) suke nema? Kuma wane ne mafi kyau ga hukunci daga Allah sabõda mutãne waɗanda suke yin yaƙĩni ( tabbataccen ĩmãni ) ?
( 1 ) Allah. Kuma Mun bai wa kowa shari'õ'insa da dõkõkinsa sa'an nan kuma da hanyar da ake bi wajen zartar da shari'ar.
( 2 ) Hukuncin Jahiliyya shi ne wanda ake ginawa a kan son rai da al'ãda da kuma ra'ayin azzalumai, ba ya da wani asali daga wani littafi na Allah.