Hausa translation of the meaning Page No 142

Quran in Hausa Language - Page no 142 142

Suratul Al-An'am from 111 to 118


111. Kuma dã a ce, lalle Mũ Mun saukar da Malã'iku zuwa gare su, kuma matattu suka yi musu magana, kuma Muka tãra dukkan kõme a kansu, gungu- gungu, ba su kasance sunã iya yin ĩmãni ba, sai fa idan Allah Yã so, Kuma amma mafi yawansu sunã jãhiltar haka.
112. Kuma kamar wancan ne Muka sanya wa kõwane Annabi maƙiyi; shaiɗãnun mutãne da aljannu, sãshensu yanã yin ishãra ( 1 ) zuwa sãshe da ƙawãtaccen zance bisa ga rũɗi. Kuma dã Ubangijinka Yã so, dã ba su aikatã shi ba, don haka ka bar su da abin da, suke ƙirƙirãwa.
113. Kuma dõmin zukãtan waɗanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba su karkata saurãrẽ zuwa gareshi, kuma dõmin su yarda da shi, kuma dõmin su kamfaci abin da suke mãsu kamfata.
114. Shin fa, wanin Allah nake nẽma ya zama mai hukunci, alhãli kuwa Shĩ ne wanda Ya saukar muku da Littãfi abin rabẽwadaki- daki? Kuma waɗanda Muka bai wa Littãfi sunã sanin cẽwa lalleshi ( Alƙur'ãni ) abin saukarwa ne daga Ubangijinka, da gaskiya? Sabõda haka kada ku kasance daga mãsu shakka.
115. Kuma kalmar Ubangijinka tã cika, tanã gaskiya ( 2 ) da ãdalci. Babu mai musanyãwa ga kalmõminSa, kuma Shi ne Maiji, Masani.
116. Kuma idan ka bi mafiya yawan waɗanda suke a cikin ƙasa da ɗã'a sunã ɓatar da kai daga hanyar Allah. Ba su bin kõme sai fãce ƙaddari- faɗi ( 3 ) suke yi.
117. Lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Mafi sani ga wanda yake ɓacẽwa daga hanyarsa kuma Shi ne mafi sani ga masu shiryuwa.
118. Sabõda haka ku ci daga abin da aka ambaci sũnan Allah ( 4 ) kansa, idan kun kasance mãsu ĩmãni da ãyõyinSa.
( 1 ) Wahayin shaiɗãnu sãshensu zuwa ga sãshe da ƙãwata ƙarya ta zama kamar gaskiya. Kamar Shaiɗan ya sanya wasiwãsi: Dã da'awar Annabi gaskiya ce: Ai dã manyan mutãne ne zã su fãra bin ta, ba matalautã ba, kõ kuwa annabi mai sihiri ne dõmin yanã raba miji da mãta, da ɗa da uba. Watau su karkatar da magana, dõmin su karkatar da wãwãye daga bin gaskiya.
( 2 ) Musulunci kõ Alƙur'ãni ne cikon addinin Allah, babu mai iya zõwa da wani abu sãbo kõ ya ƙãra wani abu a cikinsata kõwace hanya kuma bãbu mai iya musanya wani abu acikinsa. Ya cika ya kammala, sai biya kawai. Annabi ya ce: « Wanda ya yi wani aiki ba da umuruinsa a kan abin da ya aikata ɗin nan ba, to, an mayar masa; ba a karɓaba. »
( 3 ) Kamar maganarsu cẽwa mũshe wanda Allah da kansa Ya kashe, ya fi dãcẽwa da a ci shi, bisa ga abin da mutãne suka yanka.
( 4 ) An sani daga nan cẽwa ambaton sũnan Allah wajen yankan dabba wãjibi ne, idan yankansa ba. an tuna. Wanda ya manta, anã cin yankansa, amma wanda ya bari da gangan, bã zã a ci yankansa ba.