Hausa translation of the meaning Page No 25

Quran in Hausa Language - Page no 25 25

Suratul Al-Baqarah from 164 to 169


164. Lalle ne, a cikin halittar sammai da ƙasa, da sãɓãwar dare da yini, da jirãge wadaɗnda suke gudana a cikin tẽku ( ɗauke ) da abin da yake amfãnin mutãne, da abin da Allah Ya saukar daga sama daga ruwa, sai Ya rãyar da ƙasa da shi a bãyan mutuwarta, kuma Ya wãtsa, a cikinta, daga dukan dabba, kuma da jũyãwar iskõki da girgije hõrarre a tsakãnin sama da ƙasa; haƙĩƙa, akwaiãyõyi ga mutãne mãsu yin hankali.
165. Kuma akwai daga mutãne wanda yake riƙon kinãye, baicin Allah, suna son su, kamar son Allah, kuma waɗanda suka yi ĩmãni ne mafiya tsananin so ( 1 ) ga Allah. Kuma dã waɗanda ( 2 ) suka yi zãlunci, suna ganin lõkacin da zã su ga azãba, da cewa lalle ne ƙarfi ga Allah yake duka, da cẽwa lalle neAllah Mai tsananin azãba ne.
166. A lõkacin da waɗanda aka bi suka barranta daga waɗanda suka bi, kuma suka ga azãba, kuma sabubba suka yanke da su.
167. Kuma waɗanda suka bi, suka ce: « Dã lalle ne muna da wata kõmãwa ( dũniya ) sai mu barranta dagagare su kamar yadda suka barranta daga gare mu ( dã ba su riƙi kinãyen ba ) . » Kamar wancan ne Allah ke nũna musu ayyukansu, suna da nadãmõmi a kansu, kuma ba su zama mãsu fita daga wutar ba.
168. Yã ku mutãne! ( 3 ) Ku ci daga abin da yake a cikin ƙasa, wanda yake halal, mai dãɗi. Kuma kada ku bi zambiyõyin ( 4 ) Shaiɗan. Lalle ne shi, gare ku, maƙiyi ne bayyananne.
169. Yana umurnin ku ne kawai da mugun aiki da alfãsha, kuma da ku faɗi abin da ba ku sani ba ga Allah.
( 1 ) So mai kai ga karɓar umurnidaga abin son, wanda ba Allah ba shi ne shirki da kãfirci.Amma so sabõda ihsãnin abin son, kõ dõmin zamansa sãlihi dõmin a yi kõyi da aikinsa na cikin haddõdin sharĩ'a, bã shirki ba ne, dõmin bai kai yadda mũminai ke son Allah ba.
( 2 ) Ãyõyi na l65 da l66 da 167duka ɗinke suke ga ma'anoninsu. Ãyã ta l66 zarafi ce ga ta l65, sa'an nan ta 167 an haɗa rabinta ga ãyã ta 166. Sa'an nan sauran ãyã 167 ta zama ta'aƙĩbi da bayãni gare su duka.
( 3 ) Yã kira mutãne a kan, bai ce mũminai ba, dõmin ba dukan Musulmi yake mũmini ba, sai wanda ya tsĩra daga ãyõyinda ke tafe. A cikinsu akwai abin da zai mai da Musulmi kãfiri kõ mai bidi'a.
( 4 ) Hanyõyin Shaiɗan ga halattar da abin da Allah Ya haramta kõ haramtar da abin da Allah Ya halatta dõmin kãga hukuncin da bai zo daga Allah ba, shirki ne tãre da Allah. Yã ce zambiyõyin Shaiɗan, dõmin Shaiɗan bã ya da hanya miƙaƙƙiya.