Hausa translation of the meaning Page No 49

Quran in Hausa Language - Page no 49 49

Suratul Al-Baqarah from 283 to 286


283. Kuma idan kun kasance a kan tafiya, kuma ba ku sami marubũci ba, to, a bãyar da jingina karɓaɓɓiya ( ga hannu ) . To, idan sãshenku ya amince wa sãshe, to, wanda aka amincẽ wannan sai ya bãyar da amãnarsa, kuma ya bi Allah, Ubangijinsa, da taƙawa. Kuma kada ku ɓõye shaida, kuma wanda ya ɓõye ta, to, shi mai zunubin zũciyarsa ne. KumaAllah ga abin da kuke aikatãwa Masani ne.
284. Allah ne, da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, kuma idan kun bayyana abin da yake a cikin zukatanku ( na shaida ) , ko kuka ɓõye shi, Allah zai bincike ku da shi, sa'an nan Ya yi gãfara ga wanda Yake so, kuma Ya azabta wanda Yake so. Kuma Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne. ( 1 )
285. Manzon Allah yã yi ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare shi daga Ubangijinsa, da mũminai. Kõwanensu yã yi ĩmãni da Allah, da mala'ikunSa, da littattafanSa, da manzanninSa. Bã mu rarrabẽwa a tsakãnin daya daga manzanninSa. Kuma ( mũminai ) suka ce: « Mun ji kuma mun yi dã'a; ( Muna nẽman ) gãfararKa, yã Ubangijinmu, kuma zuwa a gare Ka makõma take ( 2 ) »
286. Allah ba Ya kallafa wa rai fãce ikon yinsa, yana da lãdar abin da ya tsirfanta, kuma a kansa akwai zunubin abin da ya yi ta aikatãwa: « Yã Ubangijinmu! Kada Ka kãmã mu, idan mun yi mantuwa, ko kuma mun yi kuskure. Yã Ubangijinmu! Kuma kada Ka aza nauyi a kanmu, kamar yadda Ka aza shi a kan waɗanda suke a gabãninmu. Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanya mu ɗaukar abin da bãbu ĩko gare mu da shi. Kuma Ka yãfe daga gare mu, kuma Ka gãfarta mana, kuma Ka yi jin ƙai gare mu. Kai ne Majibincinmu, sabõda haka Ka taimake mu a kan mutãnen nan kãfirai. »
( 1 ) Wannan ãyã ita ce ƙarshen bayãni a kan bãyar da shaida. A kan shaidar da mutum ya bayyana kõ ya ɓõye a cikin rai, Allah Yake yi masa bincike dõmin hakkin wani da ya rãtaya a kan wannan bayyanawar kõ ɓõyewar. Ita ayar da biyu na bayanta sun ƙunshi ilmin Baƙara dukanta.
( 2 ) Aya ta 285 da ta 286 sun ƙunshi aikin Annabi da waɗanda suka bi shi daga aƙidada magana da aiki da kyautatãwa da mayar da al'amari gaAllah, da addu'ar tsari da nema daga Ubangijinsu. Aya ta286 ita ce mafi kyaun addu'a. Kuma ta nũna Musulmi sun sãɓa wa Yahũdãwa mãsu cewa 'Mun ji, munƙi!'