Hausa translation of the meaning Page No 62

Quran in Hausa Language - Page no 62 62

Suratul Al-Imran from 92 to 100


92. Bã zã ku sãmi kyautatãwa ba, sai kun ciyar daga abin da kuke so. Kuma abin da kuka ciyar, kõ mẽne ne, to, lalle ne Allah,gare shi, Masani ne.
93. Dukan abinci yã kasance halal ne ga Bani lsrã'ĩla, fãce abinda Isrã'ĩla ya haramta wa kansadaga gabãnin saukar da Attaura. Ka ce: « To, ku zo da Attaura sa'an nan ku karantã ta, idan kun kasance mãsu gaskiya ne. »
94. « To, wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah daga bãyan wannan, to, waɗannan sũ ne azzãlumai. »
95. Ka ce: « Allah Ya yi gaskiya, sabõda haka ku bi aƙĩdar Ibrãhĩma mai karkata zuwa ga gaskiya; kuma bai kasance daga mãsu shirki ba. »
96. Kuma lalle ne, Ɗaki na farko ( 1 ) da aka aza dõmin mutãne, haƙĩƙa, shi ne wanda ke Bakka ( 2 ) mai albarka kuma shiriya ga tãlikai.
97. A cikinsa akwai ãyõyi bayyanannu; ( ga misãli ) matsayin Ibrãhĩma. Kuma wanda ya shige shi yã kasance amintacce. Kuma akwai hajjin Ɗãkin dõmin Allah a kan mutãne, ga wanda ya sãmi ĩkon zuwa gare shi, kuma wanda ya kafirta to lalle Allah Mawadãci ne daga barin tãlikai.
98. Ka ce: « Ya kũ Mutãnen Littãfi! Don me kuke kãfirta da ãyõyin Allah, alhãli kuwa Allah Mai shaida ne a kan abin da kuke aikatãwa? »
99. Ka ce: « Ya ku Mutãnen Littãfi! Don me kuke taushe wanda ya yi ĩmani, daga hanyar Allah, kuma kunã nẽman ta zama karkatacciya, alhãli kuwa kunã mãsu shaida? Kuma Allah bai gushe daga abin da kuke aikatãwa ba yana Masani. »
100. Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi ɗã'aga wani ɓangare daga waɗanda aka bai wa Littãfi, zã su mayar da ku kãfirai a bãyan ĩmãninku!
( 1 ) Ɗãkunan Allah a cikin ƙasa dõmin mutãne su yi ibãda zuwa gare su biyu ne; Ka'aba aMakka da Baitil Muƙaddas. An gina Ka'aba a gabaninsa da shekara arba'in. Dãkin Bakka kuwa Ibrãhĩma ne ya gina shi alhãli Yahũdu da Nasãra sunã cẽwa kan addininsa suke. Dã sunã faɗar gaskiya dã sun kõma a gare shi gabã ɗaya.
( 2 ) Ana ce wa Makka Bakka.