Hausa translation of the meaning Page No 102

Quran in Hausa Language - Page no 102 102

Suratul Al-Nisa from 148 to 154


148. Allah bã Ya son bayyanãwa da mũnãna daga magana ( 1 ) fãce ga wanda aka zãlunta. Kuma Allah Yã kasance Mai ji, Masani.
149. Idan kun bayyana alhẽri, kõ kuwa kuka ɓõye shi, kõ kuwa kuka yãfe laifi daga cũta, to, lalle ne Allah Yã kasance Mai yãfewa, Mai ikon yi.
150. Lalle ne, waɗanda uke kãfirta da Allah da ManzonSa kuma sunã nufin su rarrabe ( 2 ) a tsakãnin Allah da manzanninSa, kuma sunã cẽwa: « Munã ĩmãni da sãshe, kuma munã kãfirta da sãshe. » Kuma sunã nufin su riƙi hanya a tsakãnin wannan.
151. Waɗannan sũ ne kãfirai sõsai, kuma Mun yi tattali, dõmin kãfirai, azãba mai walãkantarwa.
152. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da manzanninSa, kuma ba su rarrabe a tsakãnin kõwa ba daga gare su, waɗannan zã Mu bã su ijãrõrinsu, kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai.
153. Mutãnen Littãfi sunã tambayar ka ka saukar da wani littãfi daga sama, a kansu, to, lalle ne sun tambayi Mũsã mũfã girma daga wannan, suka ce: « Ka nũna mana Allah bayyane. » Sai tsãwa ta kãmã su sabõda zãluncinsu, sa'an nan kuma suka riƙi maraƙi ( abin bautãwa ) bãyan hujjoji bayyanannu sun je musu. Sa'an nan Muka yãfe laifi daga wancan. Kuma Mun bai wa Mũsã dalĩli bayyananne.
154. Kuma Muka ɗaukaka dũtse sãma da su, sabõda alkawarinsu, kuma Muka ce musu: « Ku shiga ƙõfar kunã mãsu tawãli'u, » Kuma Muka ce musu: « Kada ku ƙẽtare haddi a cikin Asabat, » kuma Muka riƙi alkawari mai kauri daga gare su. « »
( 1 ) Magana mummũna. Allah bã Ya son bayyana mugunyar magana, sai dai wanda aka zãlunta, yana iya kai ƙãra, kumayana iya yin addu'a a kan wanda ya zãlunce shi. Sa'an nan ya shiga bayyanãwar abin da ake nufi da miyagun maganganu a cikin ãyõyin da suke bin wannan.
( 2 ) Rarrabẽwa tsakãnin Allah da ManzanninSa, shi ne mutumya ce ga misãli, « Na yarda Allah gaskiya ne, zan yi dukaabin da yake mai kyau saboda Shi, amma bãbu ruwãna da wani Annabi kõ wani anzõ, » ko kuma ya ce ai duk addĩnai ɗaya ne, ana nufin Allah da su, sai mutum ya bi abin da ya ga dama. Duka irin waɗannan maganganu bã su da kyau, kãfirci ne.