Hausa translation of the meaning Page No 103

Quran in Hausa Language - Page no 103 103

Suratul Al-Nisa from 155 to 162


155. To, sabõda warwarẽwarsu ga alkawarinsu, da kãfirtarsu da ãyõyin Allah, da kisansu ga Annabãwa, bã da hakki ba, da maganarsu: « Zukãtanmu sunã cikin rufi. » Ã'a, Allah ne Ya yunƙe a kansu sabõda kãfircinsu, sabõda haka bã zã su yi ĩmãni ba fãce kaɗan.
156. Kuma sabõda kãfircinsu da faɗarsu, a kan Maryama, ƙiren ƙarya mai girma.
157. Da faɗarsu ( 1 ) : « Lalle ne mu, mun kashe Masĩhu ĩsã ɗan Maryama Manzon Allah, » alhãli kuwa ba su kashe shi ba, kuma ba su kẽre shi ba, kuma ammaan kamanta shi ne a garẽ su. Lalle ne waɗanda sauka sãɓã wa jũna a cikin sha'aninsa lalle ne, sunã shakka daga gare, shi, bã da wani ilmi fãce bin zato kuma ba su kashe shi ba bisa ga yaƙĩni.
158. Ã'a, Allah Ya ɗauke shi zuwa garẽ Shi, kuma Allah Yã kasance Mabuwãyi, Mai hikima.
159. Kuma bãbu kõwa daga Mutãnen Littafi ( 2 ) , fãce lalle yanã ĩmãni da shi a gabãnin mutuwarsa, kuma a Rãnar Ƙiyãma yana kasancẽwa mai shaida, a kansu.
160. To, sabõda zãlunci daga waɗanda suka tũba ( Yahũdu ) Muka haramta musu abũbuwa masu dãɗi waɗanda aka halatta su a gare su, kuma sabõda taushẽwarsu daga hanyar Allah da yawa.
161. Da karɓarsu ga riba, alhãli kuwa an hana su daga gare ta, da cin su ga dũkiyar mutãne daƙarya. Kuma Muka yi tattali, dõmin kãfirai, azãba mai raɗaɗi.
162. Amma tabbatattu ( 3 ) a cikin ilmi daga gare su, da mũminai, suna ĩmani da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar daga gabãninka, madalla da masu tsai da salla, da mãsu bãyar da zakka, da mãsu ĩmãni daAllah da Rãnar Lãhira. Waɗannan zã Mu bã su lãda mai girma.
( 1 ) Faɗarsu ta izgili watau suna cewa: « Mun kashe ĩsã ɗan Maryama wanda yake da'awar shi Manzon Allah ne. » Asalin maganar Yahũdu suka karkatar da Dãwũda sarkin Dimashƙa, da cewa ga wani mutum nan yana ɓãta ƙasa da aƙĩdar mutãne a Baitil Maƙdis sabõda haka ya bãyar da õda ga hãkimansa a Baitil Maƙdis da a kashe ĩsã sai suka tafi suka tsare shi a cikin gida shi da sahabbansa, watau Hawãriyawa. ĩsã ya rõki waninsu da yarda da kisa a kan sakamakon Aljanna. Sai ƙaraminsu ya yarda, Allah Ya sanya masa sifar ĩsã, a bãyan haka Ya ɗauke ĩsã. Shi kuma aka kashe shi matsayin ĩsã Daga nan,Yahũdu suna zaton sun kashe shi, kuma waɗanda suka halarci ƙissar, suka sãɓã wa jũna wajen sifar ĩsã da c ẽwa Shi ne Allah, ko ɗan Allah, ko ɗayan uku, ko manzon Allah, kamar yaddaya gabãta a cikin Baƙara.
( 2 ) An ce Mutãnen Littafi na zamanin Annabi Isa lalle suna imani da shi gabanin mutuwarsa cewa shi ba Allah ne ba, kuma ba ɗan Allah ne ba; kowannensu kamin ya mutu yana imani da cewa Isa Manzon A1lah ne, a lokaein da imanin ba ya amfanin sa. Allah Ya fi sani.
( 3 ) Kabĩla mai asali tana lãlãcewa sabõda rashin bin addini, har ta zama mafi sharrin halittar Allah, kamar Yahũdu. Kuma a cikin haka wanda ya komawa gaskiyasai ya koma ga tsohon asalin, ya ƙãra daukaka da shi, kamar waɗanda suka musulunta daga cikinsu.