Hausa translation of the meaning Page No 126

Quran in Hausa Language - Page no 126 126

Suratul Al-Ma'idah from 109 to 113


109. A ranar da Allah Yake tãra manzanni sa'an nan Ya ce: « Mene ne aka karɓa muku? » () su ce: « Bãbu ilmi a gare mu. Lalle ne Kai, Kai ne Masanin abubuwan fake. » ( 1 )
110. A lõkacin da Allah Ya ce: « Yã Ĩsã ɗan Maryama!Ka tuna ni'ima Ta a kanka, kuma a kan mahaifiyarka, a lõkacin da Na ƙarfafa ka da Rũhul Ƙudusi,kanã yiwa mutãne magana a cikin shimfiɗar jariri, da kuma kanã dattijo. Kuma a lõkacin da Na sanar da kai rubutu da hikima da Attaura da Injĩla, kuma a lõkacin da kake yin halitta daga lãkã kamar surar tsuntsu da izinĩNa, sa'an nan ka hura a cikinta sai ta zama tsuntsu da izinĩNa, kuma kanã warkar da haifaffen makaho da kuturu, da izinĩNa, kuma a lõkacin da kake fitar da matattu da izinĩNa, kuma a lõkacin da Na kange Banĩ Isrã'ĩla daga gare ka, a lõkacin da ka je musu da hujjõji bayyanannu, sai waɗanda suka kãfirta daga cikinsu suka ce: 'Wannan bã kõme ba ne, fãce sihiri bayyananne.' »
111. « Kuma a lõkacin da Na yi wahayi zuwa ga Hawãriyãwa ( 2 ) cewa ku yi ĩmãni da Ni, kuma da ManzoNa. Suka ce: » Mun yi ĩmãni, kuma ka shaida da cewa lalle mu, mãsu sallamãwa ne. « »
112. A lõkacin da Hawarãyãwa suka ce: « Ya Ĩsa ɗan Maryam! shin, Ubangijinka Yanã iyãwa Ya saukar da kaɓaki a kanmu daga samã? » ( Ĩsã ) Ya ce: « Ku bi Allah da taƙawa idan kun kasance muminai. »
113. Suka ce: « Munã nufin mu ci daga gare shi ne, kuma zukãtanmu su natsu kuma mu san cewa lalle ne, kã yi mana gaskiya, kuma mu kasance daga mãsu shaida a kansa. »
( 1 ) A nan hukunce- hukuncen alkawurra suka ƙãre a wannan sura daga ãyã ta sama da wannan. Kuma da wannan ãyã ta l09 Allah Yanã yi mana hikãyar abin da zai auku a Lãhira dabincinkenSa ga tsare alkawari, kõ rashin tsarewa. Ya fãra da AnnabãwanSa da ga Musulunci, kuma dõmin shi ne Annabi na ƙarshen da ba a manta abubuwan da mutãnensa suka yi ba a gabãnin ɗauke shi, da kuma a bãyan ɗauke shi ɗin. Ya aiko, da ƙarin bãyani a kan irin muhãwarar da zã ta shiga a tsakãninSa da Annabãwa.Yã yi misãli da Ĩsã dõmin mutanensa nã nan a cikin wannan al'umma,anã kiran su zuwa ga musulunci, kuma domin shine Annabi na ƙarshen da ba a manta abubuwan da mutanensa suka yi ba a gabaninɗauke shi ɗin.
( 2 ) Hawãriyãwa su ne sahabban Ĩsã, amincin Allah ya tabbata a gare shi. Sunã sanyãwar farãren tufãfi, dõmin haka aka yi musu suna da haka.