Hausa translation of the meaning Page No 125

Quran in Hausa Language - Page no 125 125

Suratul Al-Ma'idah from 104 to 108


104. Kuma idan aka ce musu: « Ku zo zuwa ga abin da Allah Ya saukar, kuma zuwa ga Manzo, » sai su ce: « Mai isarmu shi ne abin da muka iske ubanninmu a kansa. » Shin, kuma kõ dã ubanninsu sun kasance bã su sanin kõme kuma bã su shiryuwa?
105. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku lazimci ( 1 ) rãyukanku, wanda ya ɓace bã zai cuce ku ba idan kun shiryu, zuwa ga Allah makõmarku take gabã ɗaya. Sa'an nan Ya bã ku lãbari ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
106. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Shaidar ( 2 ) tsakãninku, idan mutuwa ta halarci ɗayanku, a lõkacin wasiyya, maza biyu ne ma'abuta ãdalci daga gare ku, kõ kuwa wasu biyu daga wasunku idan kun tafi a cikin ƙasa sa'an nan masĩfarmutuwa ta sãme ku. Kunã tsare su daga bãyan salla har su yi rantsuwa da Allah; idan kun yi shakka: « Bã mu sayen kuɗi da shi, kõ dã ya kasance ma'abucin zumunta kuma bã mu ɓõye shaidar Allah. Lalle ne mu, a lõkacin, haƙĩƙa, munã daga mãsu zunubi. »
107. To, idan aka gane cewa lalle sũ, sun cancanci zunubi to sai wasu biyu su tsayu matsayibsu daga waɗanda suka karɓa daga gare su, mutãne biyu mafiya cancanta, sa'an nan su yi rantsuwa da Allah: « Lalle ne shaidarmu ce mafi gaskiya daga shaidarsu, kuma ba mu yi zãlunci ba. Lalle mu, a lõkacin haƙĩƙa, munã daga azzãlumai. »
108. Wannan ne mafi kusantar su zo da shaida a kan fuskarta kõ kuwa su yi tsõron a tũre rantsuwõyi a bãyan rantsuwõyinsu. Kuma ku bi Allah da taƙawa kuma ku saurara, kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne fãsiƙai.
( 1 ) Wanda yake son Ya gyãra wani sai ya gyãra kansa daga farko. wanda ya gyara kansa ɓatar wani bã ta cutarsa. Ba a nufin a bar wa'azi wãtau a ƙyãle mutane da jãhilcinsu.
( 2 ) Idan husuma ta auku a tsakãnin Musulmi da tsakãnin kãfirai, kuma su kãfiran suka zama mudda'a alaihim ( waɗanda ake tuhuma ) , kuma bãbu wata shaida sai su, to, sai su yi rantsuwa a wurin ibãdarsu, a kan su ne da gaskiya, a hukumta musu da hakkin. Bayan haka, idan an sãmi wata shaida a kan ƙaryarsu ana warware hukuncin a bãyan mudda'i ( mãsu ƙãra ) biyu Musulmi sun yi rantsuwa cewa abin da waɗancan suka faɗa ƙarya ne, abin da shaidunsu suka yi shaida da shi, shi ne gaskiya.