Hausa translation of the meaning Page No 134

Quran in Hausa Language - Page no 134 134

Suratul Al-An'am from 53 to 59


53. Kuma kamar wannan ne, Muka fitini sãshensu da sãshe, dõmin su ce: « Shin waɗannan ne Allah Ya yi falala a kansu daga tsakãninmu? » Shin, Allah bai zama Mafi sani ba ga mãsu gõdiya?
54. Kuma idan waɗanda suke yin ĩmãni da ãyõyinMu suka jẽ maka, sai ka ce: « Aminci ya tabbata a gareku; Ubangjinku Ya wajabta rahama ga kanSa, cẽwa lalle ne wanda ya aikata aibi da jãhilci daga cikinku, sa'an nan kuma ya tũba daga bãyansa, kuma ya gyãra, to, lalle Shi, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. »
55. Kuma kamar wannan ne Muke bayyana ãyõyi, daki- daki, kuma dõmin hanyar mãsu laifi ta bayyana.
56. Ka ce: « Lalle ne ni, an hana ni in bauta wa waɗanda kuke kira daga baicin Allah. » Ka cc: « Ba ni bin son zũciyõyinku, ( dõmin in nã yi haka ) lalle ne, nã ɓace. A sa'an nan, kuma ban zama daga shiryayyu ba. »
57. Ka ce: « Lalle ne inã kan hujja daga Ubangjina, kuma kun ƙaryata ( ni ) game da Shi; abin da kuke nẽman gaugãwarsa, bã ya wurina, hukunci kuwa bai zama ba fãce, ga Allah, Yanã bãyar da lãbãrin gaskiya, kuma shĩ ne mafi alhẽrin mãsu rarrabẽwa. »
58. Ka ce: « Lalle ne, dã a wurina akwai abin da kuke nẽman gaugãwa da shi, haƙĩƙa dã an hukunta al'amarin, a tsakãnina da tsakãninku, kuma Allah Shĩ ne Mafi sani ga azzũlumai. »
59. Kuma a wurinSa mabũdan ( 1 ) gaibi suke, babu wanda yake sanin su fãce Shi, kuma Yanã sanin abin da ke a cikin tudu da ruwa, kuma wani ganye ba ya fãɗuwa, fãce Yã san shi, kuma bãbu wata ƙwãya a cikin duffan ƙasã, kuma babu ɗanye, kuma babu ƙẽƙasasshe, fãce yanã a cikin wani Littãfi mai bayyanãwa.
( 1 ) Lõkacin aukuwar abũbuwa na alhẽri da na azãba da rãyuwa da mutuwa dasauransu, bãbu wanda ya san su sai Allah. Wanda ya ce ya san wani abu na gaibi alhãli kuwa shĩ ba wani manzon Allah ba, to, kãfiri ne. haka kuma wanda yake cẽwa, Annabãwã sun san dukkan gaibi, kamar yadda Allah Ya sani, shĩ mã kãfiri ne.