Hausa translation of the meaning Page No 133

Quran in Hausa Language - Page no 133 133

Suratul Al-An'am from 45 to 52


45. Sai aka katse ƙarshen mutãnen, waɗanda suka yi zãlunci. Kuma gõdiya tã tabbata ga Allah Ubangijin tãlikai.
46. Ka ce: « Shin, kun gani, idan Allah Ya riƙe jinku, da gannanku, kuma Ya sanya hãtimi a kan zukãtanku, wane abin bauttãwa ne, wanin Allah, zai jẽ muku da shi? » Ka dũba yadda Muke sarrafaãyõyi, Sa'an nan kuma sũ, sunã finjirẽwa.
47. Ka ce: « Shin, kun gan ku, idan azãbar Allah ta jẽ muku, kwatsam, kõ kuwa bayyane, shin, anã halakãwa, fãce dai mutãne azzãlumai? »
48. Kuma bã Mu aikãwa da manzãnni fãce mãsu bayar da bushãra, kuma mãsu gargaɗi. To, wanda ya yi ĩmãni kuma yagyãra aiki, to, babu tsõro a kansu, kuma ba su yin baƙin ciki.
49. Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu, azãba tanã shãfar su sabõda abin da suka kasance sunã yi na fãsiƙanci.
50. Ka ce: « Ba zan ce muku, a wurina akwai taskõkin Allah ba. Kuma ba ni sanin gaibi, kuma ba ni gaya muku cẽwa ni malã'ika ne. Ba ni bi, fãce abin da ake yiwo wahayi zuwa gare ni. » Ka ce: « Shin, makãho da mai gani sunã daidaita? Shin fa, ba ku yin tunãni? »
51. Kuma ka yi gargaɗi da shi ga waɗanda suke jin tsõron a tãra su zuwa ga Ubangijinsu, ba su da wani masõyi baicinSa, kuma babu mai cẽto, tsammãninsu, sunã yin taƙawa.
52. Kuma kada ka kõri waɗanda ( 1 ) suke kiran Ubangijinsu sãfe da maraice, sunã nufin yardarSa, babu wani abu daga hisãbinsu a kanka, kuma babu wani abu daga hisãbinka a kansu, har ka kõre su ka kasance daga azzãlumai.
( 1 ) Musulunci addinin Allah ne,wanda yake faƙĩrin dũkiya da mawãdãcinta, duka ɗaya suke a gare shi. Sabõda haka wanda duka ya rigayi wani acikinsu, to, bã za a kõre shi ba dõmin ɗayan ya shiga. Allah ĩmãni Yake so, kõ daga wãne irin mutum yake, bã Ya bukãtar dũkiya.