Hausa translation of the meaning Page No 16

Quran in Hausa Language - Page no 16 16

Suratul Al-Baqarah from 102 to 105


102. Kuma suka bi abin da shaiɗãnu ( 1 ) ke karantawa a kan mulkin Sulaimãnu, kuma Sulaimãnu bai yi kãfirci ba, kuma Shaidãnun, sũ ne suka yi kãfirci, suna karantar da mutãne sihiri. Kuma ba a saukar da shi ba a kan malã'iku biyu a Bãbila, Harũta da Mãrũta. Kuma ba su sanar da kõwa ba balle su ce: « Mũ fitina kawai ne, sabõda haka kada ka kãfirta, » balle har su yi ta nẽman ilmin abin da suke rarrabẽwa tsakãnin mutum da mãtarsa da shi daga gare su. Kuma su ( mãsu yin sihirin ) ba su zama mãsu cũtar da kõwa da shi ba, fãce da iznin Allah. Kuma suna nẽman ilmin abin da yake cũtar da su, kuma bã ya amfaninsu. Kuma lalle ne, haƙiƙa, sun sani, tabbas, wanda ya saye shi, bã ya da wani rabo a cikin Lãhira. Kuma tir da abin da suka sayar da rãyukansu da shi, dã sun kasance suna sani.
103. Kuma dã lalle ne sũ, sun yi ĩmani, kuma sun yi taƙawa, haƙiƙa, da sakamako daga wurin Allah shi ne mafi alhẽri, dã sun kasance suna sani.
104. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku ce: 'Rã'inã' ( 2 ) kuma ku ce: 'Jinkirtã manã', kuma ku saurara. Kuma kãfirai suna da azãba mai raɗaɗi.
105. Waɗanda suka kãfirta daga Ma'abuta Littãfi, bã su son a saukar da wani alhẽri a kanku daga Ubangijinku, kuma mushirikai mã bã su so. Kuma Allah Yana keɓance da wanda Yake so da rahamarSa. Kuma Allah Ma'abũcin falala mai girma ne.
( 1 ) Shaiɗan shi ne dukan wanda ya san gaskiya kuma ya ƙi yin aiki da ita, mutum ne kõ aljani. Sabõda haka a nan anã nufin miyagun malamai mãsu ɗauke mutãne daga abin da Allah Ya saukar musu na addini zuwa ga abin da suke so dõmin su cũce su. Hanyar ɗauke mutãne daga addinin gaskiya ita ce a wajen jingina magana ga wanimutum sãlihi wanda aka yarda da shi a bãyan yã mutu kamar Sulaimanu, kõ kuma a jingina ta ga wanda bã zã a iya tambayarsa ba kamar malã'iku. A wannan ãyã an jinginaasalin sihiri ga Sulaimãnu aka ce da sihiri ya kai ga mulkinsa, kuma aka ce asalin sihirin nan ilmi ne daga Allah Ya saukar da shi ta kan wasu mala'iku biyu waɗanda suke a garin da ake ce wa Bãbila a ƙasar Iraƙ, anã kiransuHãrũta da Mãrũta waɗanda suke, kãfin su gaya wa mai nẽman ilmin sihirin daga gare su abin da yake so, sai sun yi masa gargaɗi da cewa: « Kada ka yi kãfirci, » sa'an nan su gaya masa abin dasuke iya raba miji da mãta da shi na sihiri. To, Allah Yã farkar da mu cẽwa Sulamiãnubai yi sihiri ba, dõmin yin sihiri kãfirci ne. Sũ mãlaman mãsu faɗin haka, sũ ne suka yi kãfirci. Mai aiki da sihiri bai cũtar kõwa sai da iznin Allah. Nẽman saninsa cũta ne, bãbu wani amfãni.
( 2 ) 'Rã'ina,' magana ce mai ma'ana iri biyu ta yabo da ta zãgi. Ta farko ita ce a lõkacin; da Annabi ke karantar da Sahabbansa sai su ce, 'ra'inã' watau dãkata mana har mu gane wannan; ta biyu ita ce, ra'inã!, watau yã ruɓaɓɓe! To, idan Sahabbai sun ce, 'ra'ina,' sunã nufin ma'anar farko, sai Yahũdu da mushirikai su jũya musu magana da ma'ana ta biyu.