Hausa translation of the meaning Page No 160

Quran in Hausa Language - Page no 160 160

Suratul Al-A'raf from 74 to 81


74. « Kuma ku tuna a lõkacin da Ya sanyã ku mamaya daga bãyan Ãdãwa kuma Ya zaunar da ku a cikin ƙasa, kunã riƙon manyan gidãje daga tuddanta, kuma kunã sassaƙar ɗãkuna daga duwãtsu; sabõda haka ku tuna ni'imõmin Allah, kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa kuna mãsu fasãdi. » ( 1 )
75. Mashawarta waɗanda suka yi girman kai daga mutanensa suka ce ga waɗanda aka raunanar, ( 2 ) ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare su: « Shin, kunã sanin cẽwaSãlihu manzo ne daga Ubangijinsa? » Suka ce: « Lalle ne mũ, da abin daaka aiko shi, mãsu ĩmãni ne. »
76. Waɗanda suka yi girman kai suka ce: « Lalle ne mu, ga abin da kuka yi ĩmãni da shi kãfirai ne. »
77. Sai suka sõke rãƙumar, kuma suka kangare daga barin umurnin Ubangijinsu, kuma suka ce: « Yã Sãlihu! Ka zõ mana da abin da kake yi mana wa'adi da shi, idan kã kasance daga manzanni ! »
78. Sai tsãwa ta kãmã su, sabõda haka suka wãyi gari a cikin gidansu guggurfãne!
79. Sai ya jũya daga barinsu, kuma ya ce: « Ya mutãnena! Lalle ne, haƙĩƙa, nã iyar muku damanzancin Ubangijina. Kuma nã yi muku nasĩha kuma amma bã ku son mãsu nasĩha! »
80. Da Lũɗu, a lõkacin daya ce wa mutãnensa: « Shin, kunã jẽ wa alfãsha, bãbu kõwa da ya gabãce ku da ita daga halittu? »
81. « Lalle ne ku, haƙĩƙa kunã jẽ wa maza da sha'awa, baicin mata; Ã'a, kũ mutãne ne maɓarnata. »
( 1 ) Fasãdi kalmar Lãrabci ce, ma'anarta ɓarna. Watau an ce musu kada su yi ɓarna cikin ɓarna dõmin haka nan zai sanya ɓarnar ta game ƙasa duka har bã zã a gane mũninta ba.
( 2 ) Shugabanni suka cẽ wa mabiyansu mãsu rauni, waɗanda suka yi ĩmãni da Manzon Allah Sãlihu. Amma ba su yi magana da mãsu ƙarfin ĩmãni ba, dõmin sun yanke ƙauna daga gare su.