Hausa translation of the meaning Page No 162

Quran in Hausa Language - Page no 162 162

Suratul Al-A'raf from 88 to 95


88. Mashawarta waɗanda suka kangare daga mutãnensa, suka ce: « Lalle ne, Munã fitar da kai, Yã Shu'aibu, kai da waɗanda suka yi Ĩmãni tãre da kai, daga alƙaryarmu; kõ kuwa lalle ku kõmo a cikin addininmu. » Ya ce: « Ashe! Kuma kõ dã mun kasance mãsu ƙĩ? »
89. « Lalle ne mun ƙirƙira ƙarya ga Allah idan mun kõma a cikin addininku a bãyan lõkacin da Allah ya tsĩrar da mu daga gare shi, kuma bã ya kasancewa a gare mu, mu kõma a cikinsa, fãce idan Al1ah, Ubangijinmu Ya so. Ubangijinmu Yã yalwaci dukan kõme ga ilmi. Ga Allah muka dõgara. Yã Ubangijinmu! Ka yi hukunci a tsakãninmu da tsakanin mutãnenmu da gaskiya, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu hukunci. »
90. Kuma mashawarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa, suka ce: « Lalle ne, idan kun bi Shu'aibu haƙĩƙa kũ, a lõkacin nan, mãsu hasãra ne. »
91. Sai tsãwa ta kãma su, sabõda haka suka wãyi gari, a cikin gidansu, sunã guggurfãne.
92. Waɗanda suka ƙaryata Shu'aibu kamar ba su zauna ba a cikinta, waɗanda suka ƙaryata Shu'aibu, sun kasance sũ nemãsu hasãra!
93. Sai ya jũya daga barinsu, kuma ya ce: « Yã mutãnena! Haƙĩƙa, nã iyar muku da sãƙonnin Ubangijina, kuma nã yi muku nasĩha! To, yãya zan yi baƙin ciki a kan mutãne kãfirai? »
94. Kuma ba Mu aika wani Annabi ( 1 ) a cikin wata alƙarya ba, fãce Mun kãma mutãnenta da azãba da cũta, tsammãninsu sunã yin ƙasƙantar da kai.
95. Sa'an nan kuma Muka musanya mai kyau a matsayin mummũna, har su yi yawa, kuma su ce: « Cũta da azãba sun shãfi ubanninmu. » ( sai su kõma wa kãfirci ) . Sai Mu kãmã su kwatsam! alhãli kuwa sũ, bã su sansancẽwa. « »
( 1 ) Daga ãyã ta 94 zuwa ãyã ta l03 duka tãlĩƙi ne dõmin farkarwa ga muhimman manganganu waɗanda ƙissoshin Annabawan nan da mutãnensu suka ƙunsa kuma, aka ce haka dai sauran Annabawa da ba a faɗa ba suka zauna da mutãnensu a cikin faɗa a tsakanin gaskiya da ƙarya.