Hausa translation of the meaning Page No 168

Quran in Hausa Language - Page no 168 168

Suratul Al-A'raf from 144 to 149


144. Ya ce: « Ya Mũsã! Lalle ne Nĩ, Nã zãɓe ka bisa ga mutãne da manzanciNa, kuma da maganãTa. Sabõda haka ka riƙi abin da Nã bã ka, kuma ka kasance daga mãsu gõdiya. »
145. Kuma Muka rubũta masa a cikin alluna daga kõwane abu, wa'azi da rarrabẽwa ga dukan kõwane abu: « Sai ka riƙe su da ƙarfi, kuma ka umurci mutãnenka, su yi riƙo ga abin da yake mafi kyawunsu; ( 1 ) zã Ni nũna muku gidan fãsiƙai. »
146. Zã Ni karkatar da waɗanda suke yin girman kai a cikin ƙasa, bã da wani hakki ba, daga ãyõyiNa. Kuma idan sun ga dukan ãyã, bã zã su yi ĩmãni da ita ba, kuma idan sun ga hanyar shiriya, bã zã su riƙe ta hanya ba, kuma idan sun ga hanyar ɓata, sai su riƙe ta hanya. Wancan ne, dõmin lalle ne su, sun ƙaryata da ãyõyinMu, kuma sun kasance, daga barinsu gãfilai.
147. Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu da gamuwa da Lãhira, ayyukansu sun ɓãci. Shin, ana saka musu, fãce da abin da suka kasance suna aikatãwa?
148. Kuma mutãnen Mũsã suka riƙi maraƙi, ( 2 ) jikin mutãne, yanã rũri, daga bãyan tafiyarsa, daga kãyan ƙawarsu. Shin, ba su ganĩ ba, cẽwa lalle ne shi, bã ya yi musu magana, kuma bã ya shiryar da su ga hanya, sun riƙa shi, kuma sun kasance mãsu zãlunci.
149. Kuma a lõkacin da suka yi nadãma, kuma suka ga cẽwalalle ne sũ haƙĩƙa sun ɓace, suka ce: « Haƙĩƙa, idan UbangijinMu bai yi mana rahama ba, kuma Ya gãfarta mana, lalle ne munã kasancẽwa daga mãsu hasãra. »
( 1 ) Mafi kyau daga Attaura shi ne wanda yake bayyananne; watau kada a yi aiki da abin da yake bai bayyana ba, sai da abin da ya bayyana, bayan an yarda cẽwa dukansu daga Allah suke.
( 2 ) Riƙon maraƙi shi ne bauta masa. Shĩ maraƙin an yĩ shi ne da mundãyen ƙawarsu, yanãda jiki irin na mutãne, kuma yanã rũri kamar na shãnu. Bã shi yin magana. Sun bautamasa a bãyan tafiyar Mũsã, acikin kwana gõma na ƙãrin mĩƙãtin.