Hausa translation of the meaning Page No 167

Quran in Hausa Language - Page no 167 167

Suratul Al-A'raf from 138 to 143


138. Kuma Muka ƙẽtarar da Banĩ Isra'ila ga tẽku, sai suka jẽ a kan wasu mutãne waɗanda sunã lizimta da ibãda a kan wasu gumãka, nãsu suka ce: « Yã Mũsã! Ka sanya mana wani abin bautawa kamar yadda suke da abũbuwan bautãwa » ( 1 ) Ya ce: « Lalle ne kũ, mutãne ne kunã jahilta. »
139. « Lalle ne waɗannan, abin da suke a cikinsa halakakke ne, kuma abin da suka kasance sunã aikãtawa ƙarya ne. »
140. Ya ce: « Shin, wanin Allah nike nẽma muku ya zama abin bautãwa, alhãli kuwa Shĩ ( Allah ) Ya fĩfĩta ku a kan halittu? »
141. Kuma a lõkacin da Muka tsĩrar da ku daga mutãnen Fir'auna, sunã tayã muku mugunyar azãba. sunã karkashe ɗiyanku maza, kuma sunã rãyar da matanku. Kuma a cikin wancan akwai jarrabãwa daga Ubangijinku, ( 2 ) Mai girma.
142. Kuma Muka yi wa'adi ga Mũsã da dare talãtin ( 3 ) kuma Muka cikã su da gõma, sai miƙatin Ubangijinsa ya cika dare arba'in. Kuma Mũsã ya ce wa ɗan'uwansa, Hãrũna: « Ka maye mini a cikin mutãnena, kuma ka gyãra, kuma kada ka bi hanyar mãsu fasãdi. » Kuma a lõkacin da Mũsã ya jẽ ga mĩkatinMu, kuma Ubangijinsa Ya yi masa magana, shi Mũsã ya ce: « Yã Ubangijina! Ka nũna mini in yi dũbi zuwa gare Ka! » Ya ce: « Bã zã ka gan Ni ba, kuma amma ka dũba zuwa ga dũtse, to, idan ya tabbata a wurinsa, to, zã ka gan Ni. » Sa'an nan a lõkacin da Ubangijinsa, Ya kuranye zuwa ga dũtsen, Ya sanyã shi niƙaƙƙe. Kuma Mũsã ya fãɗi sõmamme. To, a lõkacin da ya farka, ya ce: « TsarkinKa ya tabbata! Nã tũba zuwa gare Ka, kuma ni ne farkon mũminai. »
( 1 ) Farkon faɗan ƙarya da gaskiya a tsakãnin Banĩ Isra'ilada Mũsã wajen son kõmawa ga al'ãdu da ƙãri a cikin addini ta hanyar bidi'a.
( 2 ) Lamĩrin Musulmi ne waɗanda ake yi wa magana yanzu a harshen Muhammadu, domin su wa'aztu da labarun mutanen farko.
( 3 ) Ƙissõshin da ke tafe daga nan, suna nũna hani ga a ƙãra wani abu a cikin umarnin Allah. Kõwane irin ƙãri shi ne ake cẽwa bidi' a, kuma kõ dã an yi shi ne da nufin ƙwarai. Bidi'a tanã kãwo fitina ga mãsu ita.
143.