Hausa translation of the meaning Page No 218

Quran in Hausa Language - Page no 218 218

Suratul Yunus from 79 to 88


79. Kuma Fir'auna ya ce: « Ku zo mini da dukan masihirci, masani. »
80. To, a lõkacin da masihirta suka je, Mũsã ya ce musu, « Ku jẽfa abin da kuke jẽfãwa. »
81. To, a lõkacin da suka jẽfa, Mũsa ya ce: « Abin da kuka zo da shi sihiri ne. Lalle ne Allah zai ɓãta shi. Haƙĩƙa Allah bã Ya gyãra aikin maɓarnata. »
82. « Kuma Allah Yanã tabbatar da gaskiya da kalmõminSa, kõ dã mãsu laifi sun ƙi. »
83. Sa'an nan bãbu wanda ya yi ĩmãni da Mũsa fãce zuriya daga mutãnensa, a kan tsõron kada Fir'auna da shũgabanninsu su fitinẽ su. Lalle, haƙĩƙa, Fir'auna marinjãyi ne a cikin ƙasa, kuma lalle shĩ haƙĩƙa, yanã daga mãsu ɓarna.
84. Kuma Mũsã ya ce: « Yã kũ mutãnena! Idan kun kasance kun yi ĩmãni da Allah, to, a gare Shi sai ku dõgara, idan kun kasance Musulmi. »
85. Sai suka ce: « Ga Allah muka dõgara. Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanyã mu fitina ga mutãne azzãlumai. »
86. « Kuma Ka kuɓutar da mu dõmin RahamarKa, daga mutãne kãfirai. »
87. Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã da ɗan'uwansa, cẽwa: Kũ biyu, ku zaunar da mutãnenku a Masar a cikin wasu gidãje. Kuma ku sanya gidãjenku su fuskanci Alƙibla ( 1 ) , kuma ku tsayar da salla. Kuma ku bãyar da bushãra ga mãsu ĩmãni.
88. Sai MũSã ya ce: « Yã Ubangijinmu! Haƙĩƙa Kai ne Ka bai wa Fir'auna da majalisarsa ƙawa da dũkiyõyi a cikin rãyuwar dũniya, yã Ubangijinmu, dõmin su ɓatar ( damutãne ) daga hanyarKa. Yã Ubangijinmu! Ka shãfe a kan dũkiyarsu kuma Ka yi ɗauri ( 2 ) a kan zukãtansu yadda bã zã su yi ĩmãni ba har su ga azãba mai raɗaɗi. »
( 1 ) Su sanya gidãjensu sunã fuskantar Alƙibla ta Ka'aba dõmin su riƙa yin salla a cikin gidãjen, sabõda tsõron in sun tafi masallaci zã a fãɗa su da dũka sunã a cikin salla. Wannan kuma yã nũna yadda ake son gidajen Musulmi su kasance a kõ da yaushe.
( 2 ) Mũsã ya yi addu'a a kansu, har da rashin ĩmãni sabõda yã sãmi lãbãrin bã zã su yi imãni ba, kamar mutãnen Nũhu.