Hausa translation of the meaning Page No 217

Quran in Hausa Language - Page no 217 217

Suratul Yunus from 71 to 78


71. Kuma ka karanta musu lãbãrin Nũhu, a lõkacin da ya ce wa mutãnensa, « Ya mutãnẽna! Idan matsayĩna da tunãtarwata ameda ãyõyin Allah sun kasance sun yi nauyi a kanku, to, ga Allah na dõgara. Sai ku tãra al'amarinku, kũ da abũbuwan shirkinku, sa'annan kuma kada al'amarinku ya kasance rufaffe a kanku, sa'an nan kuma ku kashe ni, kada ku yi mini jinkiri. »
72. « Kuma idan kuka jũya bãya, to, ban tambaye ku wata ijãra ba. ljãrata ba ta zama ba fãce daga Allah, kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu sallamãwa. » ( 1 )
73. Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan Muka kuɓutar da shi da wanda yake tãre da shi, a cikin jirgi, kuma Muka sanya su mãsu mayẽwa, kuma Muka nutsar da waɗanda suka ƙaryata ãyõyinMu. Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance.
74. Sa'an nan kuma Muka aika waɗansu Manzanni daga bãyansa zuwa ga mutãnensu, suka jẽmusu da hujjõji bayyanannu, to, ba su kasance zã su yi ĩmãni ba sabõda sun ƙaryata shi a gabani. Kamar wannan ne Muke rufẽwa a kan zukãtan mãsu ta'addi.
75. Sa'an nan kuma a bãyansu Muka aika Mũsa da Hãrũna zuwa ga Fir'auna da mashãwartansa, tãre da ãyõyinMu. Sai suka kangara kuma sun kasance mutãne mãsu laifi.
76. Sa'an nan a lõkacin da gaskiya ta jẽ musu daga gare Mu, suka ce: « Wannan haƙĩƙa sihiri ne bayyananne. »
77. Mũsã ya ce: « Shin, kunã cẽwa ga gaskiya a lõkacin data zo muku? Shin, sihiri ne wannan? Lalle masihirci, bã ya cin nasara. »
78. Suka ce: « Shin, ka zo mana ne dõmin ka jũyar da mu daga abin da muka iske ubanninmu a kansa, kuma girma ya kasance gare ku, ku biyu a cikin ƙasa? Bã zã mu zama mãsu ĩmãni ba sabõda ku. »
( 1 ) Watau dukan abin da na zomuku da shi na umurni kõ hani, to, ni ma an umurce nida yinsa kõ barinsa. Kuma bã ni nẽman wata ijãrar karantarwa daga gare ku dõmin Allah Ya umarce ni da iyar da manzancinsS zuwa gare ku, sabõda haka Shi ne zai biyã ni tsãdar aikĩna.