Hausa translation of the meaning Page No 227

Quran in Hausa Language - Page no 227 227

Suratul Hud from 46 to 53


46. Ya ce: « Yã Nũhu! Lalle ne shi bã ya a ciki iyãlanka, lalle ne shĩ, aiki ne wanda ba na ƙwarai ba, sabõda haka kada ka tambaye Ni abin da bã ka da ilmi a kansa. Haƙĩƙa, Nĩ Inã yi maka gargaɗi kada ka kasance daga jãhilai. »
47. Ya ce: « Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, inã nẽman tsari gare Ka da in tambaye Ka abin da bã ni da wani ilmi a kansa. Idan ba Ka gãfarta mini ba, kuma Ka yi mini rahama, zan kasance daga mãsu hasãra. »
48. Aka ce: « Ya Nũhu! Ka sauka da aminci da, a gare Mu da albarka a kanka, kuma rahama ta tabbata a kan waɗansu al'ummõmi daga waɗanda suke tãre da kai. Da waɗansu al'ummõmi da zã Mu jiyar da su dãɗi, sa'an nan kuma azãba mai raɗaɗi ta shafe su daga gare Mu. »
49. Waccan ƙissa tanã daga lãbãran gaibi, Munã yin wahayinsu zuwa gare ka ( Muhammadu ) . Ba ka kasance kanã sanin su ba, haka kuma mutãnenka ba su sani ba daga gabãnin wannan. Sai ka yi haƙuri. Lalle ne ãƙiba tanã ga mãsu taƙawa,
50. Kuma zuwa ga Ãdãwa, ( Mun aika ) ɗan'uwansu Hũdu. Ya ce: « Yã kũ mutãnena! Ku bauta wa Allah. Ba ku da wani abin bautãwa fãce Shi. Ba ku kasance ba fãce kunã mãsu ƙirƙirãwa. »
51. « Yã ku mutãnena! Bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa, ijãrata ba ta zama ba, fãce ga wanda Ya ƙãga halittata. Shin fa, bã ku hankalta? »
52. « Kuma, ya mutãnena! Ku nẽmi Ubangijinku gãfara, sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare Shi,zai saki sama a kanku, tanã mai yawan zubar da ruwa, kuma Ya ƙãra muku wani ƙarfi ga ƙarfinku. Kuma kada ku jũya kunã mãsu laifi. »
53. Suka ce: « Yã Hũdu! Ba ka zo mana da wata hujja bayyananna ba, kuma ba mu zama mãsu barin abũbuwan bautawarmu ba dõmin maganarka, kuma ba mu zama mãsu yin ĩmãni da kai ba. »