Hausa translation of the meaning Page No 23

Quran in Hausa Language - Page no 23 23

Suratul Al-Baqarah from 146 to 153


146. Waɗanda Muka bã su Littãfi, suna saninsa kamar yadda suke sanin ɗiyansu. Kuma lalle ne wani ɓangare daga gare su, haƙiƙa, suna ɓõyewar gaskiya alhãli kuwa sũ, suna sane.
147. Gaskiya daga Ubangijinka ( 1 ) take sabõda haka, lalle kada ka kasance daga mãsu shakka.
148. Kuma kõwane ɓangare yana da alƙibla wadda yake shi mai fuskantar ta ne. Sai ku yi tsẽre zuwa ga ayyukan alhẽri, inda kuka kasance duka Allah zai zo da ku gabã ɗaya. Lalle ne Allah, a kan kõme, Mai ĩkon yi ne.
149. Kuma daga inda ka fita, to, sai ka jũyar da fuskarka a wajen Masallãci Tsararre kuma lalle tabbas, shi ne gaskiya daga Ubangijinka. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da kuke aikatãwa ba.
150. Kuma daga inda ka fita, to, ka jũyar da fuskarka a wajen Masallãci Tsararre kuma inda kuke duka, to, ku jũyar da fuskõkinku a wajensa, dõmin kada wata hujja ta kasance ga mutãne a kanku, fãce waɗanda suka yi zãlunci daga gare su. Sabõda haka kada ku ji tsõronsu kuma ku ji tsõrõNa kuma dõmin In cika ni'imaTa a kanku, kuma tsammãninku zã ku shiryu.
151. Kamar ( 2 ) yadda Muka aika Manzo a cikinku, daga gare ku, yana karanta ãyõyinMu a gare ku kuma yana tsarkake ku, kuma yana sanar da ku Littãfi da hikima, kuma yana sanar da ku abin da ba ku kasance kuna sani ba.
152. Sabõda haka, ku tuna Ni, In tunã ku, kuma ku yi gõdiya gare Ni, kuma kada ku butulce Mini.
153. Ya ku waɗanda ( 3 ) suka yi ĩmãni! Ku nẽmi taimako da haƙuri game da salla. Lalle ne, Allah na tãre da mãsu haƙuri.
( 1 ) Jũyãwar alƙibla abu ne na gaskiya daga Allah dõmin rarrashin wanda Allah bai yi nufi da tsĩrarsa ba ya ƙãre. Bãyan rarrashi sai yankẽwa wannan shi ne matakin farko da Musulmi suka fara tsiraita da shi daga maƙiyansu bayyane. Yanzu kuma Musulmi sun zama dabam.
( 2 ) Jũyar da alƙibla da yankẽwa daga dukkan kãfirai da hani daga tsõronsu kuma Allah Ya farkar da Musulmi ga ni'imõmin da Ya yi musu game da aiko Annabi daga gare su, zuwa gare su, a cikinsu, dõmin ya tsarkake su, bayyane da ɓõye, daga dukan ƙurar kãfirci. Wannan ya nũna cẽwa sai an yi rarrashin mutãne wajen kira zuwa ga addini da kõwace hanya mai yiwuwa. Bãyan haka a yanke wa wanda ya ƙi bin gaskiya bayyane kuma kadaa ji tsõronsa. Kuma aka umurce su da fuskanta zuwa ga Allah kawai da tunãwa gare Shi da gõdiya, da nisantar kafirci.
( 3 ) Magana kuma ta fuskanta zuwa ga mũminai kawai dõmin a shirya zamansu.