Hausa translation of the meaning Page No 22

Quran in Hausa Language - Page no 22 22

Suratul Al-Baqarah from 142 to 145


142. Wãwãye daga mutãne zã su ce: Mẽne ne ya jũyar da su daga alƙiblarsu wadda suka kasance a kanta? Ka ce: « Allah Ɗai ne Yake da gabas da yamma, Yana shiryar da wanda Yake so zuwa ga hanya madaidaiciya. »
143. Kuma kamar wancan, Muka sanya ku al'umma matsakaiciya ( 1 ) dõmin ku kasance mãsu bãyar da shaida a kan mutãne. Kuma Manzo ya kasance mai shaida a kanku. Kuma ba Mu sanya Alƙibla ( 2 ) wadda ka kasance a kanta ba, fãce dõmin Mu san wanda yake biyar Manzo daga wanda yake jũyãwa a kan duga- dugansa. Kuma lalle ne, tã kasance haƙĩƙa, mai girma, sai a kan waɗanda Allah Ya shiryar. Kuma ba ya yiwuwa ga Allah Ya tõzartar da ĩmãninku. ( 3 ) Lalle ne, Allah, ga mutãne, haƙĩƙa, Mai tausayi ne, Mai jin ƙai.
144. Lalle ne, Muna ganin jujjũyãwar fuskarka a cikin sama. To, lalle ne, Mu jũyar da kai ga Alƙibla wadda kake yardã da ita. Sai ka jũyar da fuskarka wajen Masallãci Tsararre, kuma inda duk kuka kasance, to, ku jũyar da fuskõkinku jiharsa. Kuma lalle ne waɗanda aka bai wa Littãfi, haƙĩƙa su, sunã sanin lalle ne, shĩ ne gaskiya, daga Ubangijinka. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da suke aikatãwa.
145. Kuma hakĩka, idan ka je wawaɗanda aka bai wa Littafi da dukan ãyã, bã zã su bi Alƙiblarka ba, kuma kai ba ka zama mai bin Alƙiblarsu ba, kuma sãshensu bã mai bin Alƙiblar ( 4 ) sãshe ba ne. Kuma haƙĩƙa, idan ka bi son zũciyõyinsu daga bãyan abin da ya zo maka daga ilmi, lalle ne kai, sa'an nan, haƙiƙa, azzãlumi kake.
( 1 ) Ãdilai, kõ matsakaita ga kõmai, babu zurẽwa,babu kãsawa ga addini da rãyuwa da sauran mu'ãmalõli duka.
( 2 ) A lõkacin da Annabi ya yi hijira zuwa Madĩna, alhãli a cikin mutãnenta akwai YahũduAllah Ya umurce shi da ya fuskanci Baitil Maƙdis. Sai Yahũdu suka ji dãɗi. Sai Manzon Allah ya fuskance ta wata gõma sha wani abu kuma Manzon Allah ya kasance yana son Alƙiblar lbrãhĩm kamar yadda ya gabata ga ãyã ta 115. Kuma ya kasance yana addu'a yanã dũbi zuwa ga sama, har Allah Ya saukar da hukuncin jũyãwa zuwa gare ta.
( 3 ) Ĩmãninku watau sallarku da kuka yi wajen Baitil Makdis, dõmin kun yi ta ne a kan umurnin Allah da ĩmãni da Shi.
( 4 ) Alƙiblar Yahũdu ita ce falalen dũtsen da ke Baitil Maƙdis. Kuma ita ce Alƙiblar Nasãra a zãmanin Ĩsã. A bãyansa Alƙiblarsu ta kõma ga mafitar rãnã, da ƙãgensu sabõda St. Paul koõ Bulis el Ƙissi, ya ce musu bãyan an ɗauke Ĩsa cẽwa: « Nã haɗu da Ĩ>sa yã ce mini lalle ne ranã tauraro ne wanda yake inã sonsa. Yanã kai gaisuwata a cikin kõwane yini sabõda haka ka umurci mutãnena, su fuskanta zuwa gare ta. » Da haka ya karkatar da su daga alƙiblarsu. Kuma inã zaton haka abin yake ga girmamãwar Lahadi maimakon Asabar dõmin Rũmãwa, ranã suke bauta wa a rãnar Lahadi wannan kuwa shi ne ma'anar « Sunday » da Tũrancin, watau 'yinin rãna.'