Hausa translation of the meaning Page No 231

Quran in Hausa Language - Page no 231 231

Suratul Hud from 82 to 88


82. Sa'an nan a lõkacin da umurninMu ya je, Muka sanya na samanta ya zama na ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu a kanta ( ƙasar Lũɗu ) daga taɓocũrarre.
83. Alamtacce a wurin Ubangijinka. Kuma ita ( ƙasar Lũɗu ) ba ta zama mai nĩsa ba daga azzãlumai ( kuraishãwa ) .
84. Kuma zuwa ga Madyana ( Mun aika ) ɗan'uwansu ( 1 ) Shu'aibu. Ya ce: « Ya Mutãnena! Ku bauta wa Allah. Ba ku da wani abin bautãwa fãce shi kuma kada ku rage mũdu da sikẽli. Lalle nĩ, inã ganin ku da wadãta. ( 2 ) Kuma lalle inã ji muku tsõron azãbar yini mai kẽwayẽwa. »
85. « Ya mutãnẽna! Ku cika mũdu da sikẽli da ãdalci, kuma kada ku naƙasta wa mutãne kãyansu, kuma kada ku yi ɓarnã a cikin ƙasa kunã mãsu fasãdi. »
86. « Falalar Allah mai wanzuwa ita ce mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance muminai, kuma ni bã mai tsaro ne a kanku ba. »
87. Suka ce: « Yã Shu'aibu! Shin sallarka ce take umurtar ka ga mu bar abin da ubanninmu suke bautãwa, kõ kuwa mu bar aikata abin da muke so a cikin dũkiyõyinmu? Lalle, haƙĩƙa kai ne mai haƙuri shiryayye! »
88. Ya ce: « Ya mutãnena! Kun gani idan no kasance a kan hujja bayyananniya daga Ubangijina, kuma Ya azurta nĩ da arzikimai kyãwo daga gare Shi? Kuma bã ni nufin in sãɓa muku zuwa ga abin da nake hana ku daga gare shi. Bã ni nufin kõme fãce gyãrã, gwargwadon da na sãmi dãma. Kuma muwãfaƙãta ba ta zama ba fãce daga Allah. A gare shi na dõgara, kuma zuwa gare Shi na wakkala. »
( 1 ) Lãrabãwa ne, sunã zaune a tsakãnin Hijaz da Shãm.
( 2 ) Inã ganin ku a cikin wadãta;bã ku da bukãtar rage wa mutãne kãyansu. Sabõda haka ku yi adalci ga mutãne wajen ciniki ya fi muku alhẽri daga dũkiyar haram mai ƙãrewa kõme yawanta.