Surah Hood | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 230
Suratul Hud from 72 to 81
72. Sai ta ce: « Yã kaitõna! Shin, zan haihu ne alhãli kuwa inã tsõhuwa, kuma ga mijĩna tsõho ne? Lalle wannan, haƙĩƙa, abu ne mai ban mãmãki. »
73. Suka ce: « Shin kinã mãmaki ne daga al'amarin Allah? Rahamar Allah da albarkarSa su tabbata a kanku, ya mutãnen babban gida! Lalle ne Shĩ abin gõdewa ne, Mai girma. »
74. To, a lõkacin da firgita ta tafi daga Ibrãhĩm, kuma bushãra tã je masa, Yanã mai jayayya a gare Mu, sabõda mutãnen Lũɗu!
75. Lalle Ibrãhĩm, haƙĩƙa mai haƙuri ne, mai yawan addu'a, mai tawakkali.
76. Ya Ibrãhĩm! Ka bijira daga wannan. Lalle shi, haƙĩƙa, umurnin Ubangijinka ne ya zo, kuma lalle ne sũ, abin da yake mai je musu azãba ce wadda bã a iya hanãwa.
77. Kuma a lõkacin da manzanninMu suka je wa Lũɗu aka ɓãta masa rai game da su, ya, ƙuntata rai sabõda su. Ya ce: « Wannan yini ne mai tsananin masĩfa. »
78. Kuma mutãnensa suka je masa sunã gaggãwa zuwa gare shi, kuma a gabãni, sun kasance sunã aikatãwar mũnãnan ayyuka. Ya ce: « Yã mutãnẽna! waɗannan, 'yã'yã na ( 1 ) sũ ne mafiya tsarki a gare ku. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku wulãkantã ni a cikin bãƙĩna. Shin, bãbu wani namiji shiryayye daga gare ku? »
79. Suka ce: « Lalle, haƙĩƙa kã sani, bã mu da wani hakki a cikin 'ya'yanka, kuma lalle kai haƙĩƙa, kanã sane da abin da muke nufi. »
80. Ya ce: « Dã dai inã da wani ƙarfi game da ku, kõ kuwa inã da gõyon bãya daga wani rukuni ( 2 ) mai ƙarfi? »
81. ( Manzannin ) Suka ce: « Yã Lũɗu! Lalle mũ, manzannin Ubangijinka ne. Bã zã su iya sãduwa zuwa gare ka ba. Sai ka yi tafiyarka a wani yankin dare da iyãlinka, kuma kada wani daga gare ku ya waiwaya fãce mãtarka. Lalle ne abin da ya same su mai sãmunta ne. Lalle wa'adinsu lõkacin sãfiya ne. Shin lõkacin sãfiya bã kusa ba ne? »
( 1 ) 'Ya'yansa- Yanã nufin mãtan aurensu, dõmin kõwane Annabi uban al'ummarsa ne.Bã ya kamãta a ce wai yanã kiran mazan gari zuwa ga 'ya'yansa uku, dõmin bãbu wata shari'a ta Allah, ga saninmu, wadda ta halattã haɗuwar mazã biyu ko fiye da biyu a kan auren mace guda.
( 2 ) Ya faɗi haka dõmin bã shi da dangi a cikinsu. Daga gare shi ba a koma aiko wani Annabi ba sai a cikin wadãtar danginsa.