Hausa translation of the meaning Page No 259

Quran in Hausa Language - Page no 259 259

Suratul Ibrahim from 25 to 33


25. Tanã bãyar da abincinta a kõwane lõkaci da iznin Ubangijinta! Kuma Allah Yanã buga misãli ga mutãne, mai yiwuwã ne, sunã tunãwa.
26. Kuma misalin kalma mummũnã ( 1 ) kamar itãciya mummũnã ce, an tumɓuke ta daga bisa ga ƙasa, bã ta da wata tabbata.
27. Allah Yanã tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni da magana tabbatacciya a cikin rãyuwar dũniya, da cikin Lãhira, Kuma Allah Yanã ɓatar da azzãlumai, kuma Allah Yanã aikata abin da Yake so.
28. Shin ba ka lura ba da waɗanda suka musanya ( 2 ) ni'imar Allah da kãfirci kuma suka saukar da mutãnensu a gidan halakã?
29. Sunã ƙõnuwa a wutar jahannama, kuma tir da matabbatarsu.
30. Kuma suka sanya wa Allah kĩshiyõyi, dõmin ɓatarwa daga hanyarSa, Ka ce: « Ku ji dãɗi, sa'an nan, lalle ne, makõmarku Wutar ce. »
31. Ka ce wa bãyĩNa waɗanda suka yi ĩmãni su tsayar da salla kuma su ciyar daga abin da Muka azurtã su,a asirce da bayyane, daga gabãnin wani wuni ya zo, bãbu ciniki a ciki, kuma bãbu abõtaka.
32. Allah ne wanda Ya halicci sammai da ƙasa kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya fitar game da shi, daga 'ya'yan itãce arziki dõminku kuma Ya hõrẽ jirgin ruwa dõmin ya yi gudu a cikin tẽku da umurninSa, kuma Ya hõrẽ muku kõguna.
33. Kuma Ya hõrẽ muku rãnã da watã sunã madawwama biyu, kuma Ya hõrẽ muku dare da wuni.
( 1 ) Kalma ta kãfirci, bã ta da asali, kamar gunar shãnu ce.
( 2 ) Kuraishãwa waRanda Allah Ya yi musu ni'imar zama a cikin hurumin Allah da aminci da Ya zuba a kansu da albarku, sun musanya gõdiya da kãfirci a lõkacin da suka ƙaryata Manzon Allah. Sun saukar da mutãnensu a gidan halaka a Badar.