Surah إبراهيم | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 258
Suratul Ibrahim from 19 to 24
19. Shin, ba ka gani ba cẽwa lalle ne Allah Yã halicci sammai bakwai da ƙasa da mallakarSa. ( 1 ) Idan Yã so zai tafiyar da ku, kuma Ya zo da wata halitta sãbuwa.
20. Kuma wancan bai zama mabuwãyi ba ga Allah.
21. Kuma suka bayyana ga Allah gabã daya, sai mãsu rauni suka ce wa waɗanda suka kangara, « Lalle ne mũ, mun kasance mãsu bi a gare ku, to, shin, kũ mãsu kãrewa ga barinmu ne daga azãbar Allah daga wani abu? » ( 2 ) Suka ce: « Dã Allah Ya shiryar da mu, dã mun shiryar da ku, daidai ne a kanmu, mun yi rãki ko mun yi haƙuri ba mu da wata mafaka. »
22. Kuma Shaiɗan ya ce a lõkacin da aka ƙãre al'amarin, « Lalle ne Allah Ya yi muku wa'adi, wa'adin gaskiyã, kuma na yi muku wa'adi, sa'an nan na sãɓã muku. Kuma bãbu wani dalĩli a gare ni a kanku fãce na kirã ku, sa'an nan kun karɓã mini. Sabõda haka kada ku zarge ni, kuma ku zargi kanku. Ban zama mai amfaninku ba, kuma ba ku zama mãsu amfãnĩna ba. Lalle na barranta da abin da kuka haɗã ni da shi gabanin wannan ( matsayi ) . Lalle azzãlumai sunã da azãba mai raɗaɗi. » ( 3 )
23. Kuma aka shigar da waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, a gidãjen Aljanna, kõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu sunã madawwamã a cikinsu da iznin Ubangijinsu, gaisuwarsu a cikinta « Salãm » , ( wãtau Aminci ) .
24. Shin, ba ka ganĩ ba, yadda Allah Ya buga wani mĩsali, kalma mai kyau ( 4 ) kamar itãciya ce mai kyau, asalinta yanã tabbatacce, kuma rẽshenta yanã cikin sama?
( 1 ) Dalĩli ne a kan kãfircin kãfirai ba ya rage mulkin Allah da kõme, domin bã su iya fita daga halittar sammai da ƙasa, waɗanda Allah Ya halitta da abin da yake mallakarsa.
( 2 ) Muhãwarar 'yan wuta a tsakãnin mabiya da shũgabannin kafirei.
( 3 ) Huɗubar Shaiɗan ga mabiyansa, a cikin wuta, a bãyan an yi muhãwara a tsakãnin mabiya da shugabannin kãfirci, sãshe yanã la'antar sãshe har abu ya kai ga Shaiɗan, watau Iblis. Shi kumaya tãshi ya yi wannan huɗuba dõmin ya ƙãra musu baƙin ciki a kan wani.
( 4 ) Kalma mai kyau ta addini tanã da asali, kamar itãciyar dabĩno ce.