Hausa translation of the meaning Page No 269

Quran in Hausa Language - Page no 269 269

Suratul Al-Nahl from 15 to 26


15. Kuma Ya jẽfa, a cikin ƙasa, tabbatattun duwatsu dõmin kada ta karkata da ku, da kõguna da hanyõyi, ɗammãninku kunã shiryuwa.
16. Kuma da waɗansu alãmõmi, kuma da taurãri sunã mãsu nẽman shiryuwa ( ga tafiyarsu ta fatauci ) .
17. Shin, wanda Yake yin halitta yanã yin kama da wanda ba ya yin halitta? Shin fa, bã ku tunãwa?
18. Kuma idan kun ƙidãya ni'imar Allah, bã ku iya lissafa ta. Lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
19. Kuma Allah Yanã sanin abin da kuke asirtãwa da abin da kuke bayyanãwa.
20. Kuma waɗanda suke kira, baicin Allah, ba su halicci kõme ba, kuma sũ ne ake halittawa.
21. Matattũ ne, bã su da rai, kuma ba su san a wane lõkaci ake tãyar da su ba.
22. Abin bautawarku, abin bautãwa ne guda, to, waɗanda ba su yin ĩmãni da Lãhira, zukãtansu mãsu musu ne, kuma su makangara ne.
23. Haƙĩƙa, lalle ne, Allah Yanã sanin abin da suke asirtãwa da abin da suke bayyanãwa. Lalle ne Shi, bã Ya Son mãsu girman kai.
24. Idan aka ce musu: « Mẽne ne Ubangijinku Ya saukar? » Sai su ce: « Tãtsũniyõyin mutãnen farko. »
25. Dõmin su ɗauki zunubansu cikakku a Rãnar Ƙiyãma, kuma daga zunuban waɗanda suke ɓatarwa bã da wani ilmi ba. To, abin da suke ɗauka na zunubi ya mũnana.
26. Lalle ne waɗanda suke a gabãninsu sun yi mãkirci, sai Allah Ya je wa gininsu daga harsãshensa, ( 1 ) sai rufi ya fãɗa a kansu daga bisansu, kuma azãba ta jẽ musu daga inda ba su sani ba.
( 1 ) Kamar yadda Allah Ya halaka Bukht Nasar. Aka halaka shi da ginin gidansa. Allah Yanã halaka kãfirai da abin da suke tãnadã wa kansu dõmin nẽman rãyuwarsu.