Hausa translation of the meaning Page No 268

Quran in Hausa Language - Page no 268 268

Suratul Al-Nahl from 7 to 14


7. Kuma sunã ɗaukar kãyanku mãsu nauyi zuwa ga wani gari, ba ku kasance mãsu isa gare shi ba, fãce da tsananin wahalar rãyuka, Lalle ne Ubangijinka ne, haƙĩƙa, Mai tausayi, Maijin ƙai.
8. Kuma da dawãki ( 1 ) da alfadarai da jãkuna, dõmin ku hau su, kuma da ƙawa. Kuma Yana halitta abin da ba ku sani ba.
9. Kuma ga Allah madaidaiciyar hanya take kuma daga gare ta akwai mai karkacẽwa. Kuma da Yã so, dã Ya shiryar da ku gabã ɗaya.
10. Shĩ ne Wanda Ya saukar da ruwa daga sama dõminku, daga gare shi akwai abin sha, kuma daga gare shi itãce yake, a cikinsa kuke yin kĩwo.
11. Yanã tsirar da shũka game da shi, dõminku zaitũni da dabĩnai da inabai, kuma daga dukan 'yã'yan itãce. Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke yin tunãni.
12. Kuma Ya hõrẽ muku dare da wuni da rãnã da watã kuma taurãri hõrarru ne da umurninSa. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke hankalta.
13. Kuma abin da Ya halitta muku a cikin ƙasa, yana mai sãɓãnin launukansa. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke tunãwa.
14. Kuma Shĩ ne Ya hõrẽ tẽku dõmin ku ci wani nama sãbõ daga gare shi, kuma kunã fitarwa, daga gare shi, ƙawã wadda kuke yin ado da ita. Kuma kuna ganin jirãge sunã yankan ruwa a cikinsa kuma dõmin ku yi nẽman ( fatauci ) daga falalarSa. Kuma mai yiwuwa ne kuna gõdẽwa.
( 1 ) Haɗa dawãki da alfadarai zuwa ga jãkuna kuma aka ce dõmin « hawansu da yin ƙawã » yana nũna cewa ba a cin dawãki da alfadarai dõmin an san cẽwa an hana cin jãkuna a lõkacin yãƙin Khaibara, kuma ãyõyin da ke gaba da wannan ãya sun nũna anã cin dabbõbin ni'ima kuma anã hawansu, kuma cin nãma yã fi hawa zama ni'ima, sabõda haka, shĩ ne ya kamãta a ambata inda ya halatta. Wannan ne mazhabar Mãliki da Ahu Hanĩfa, kuma shĩ ne maganar Abdullah bn Abbãs Allah Ya yarda da su. Wasu sun ce ana cin dawãki da alfadarai dõmin cewa, « Anã hawansu dõmin ƙawa, » bã ya hana a yi wani abu da su, wato cin nãmansu, dõmin a cikin Bukhãri daMuslim an ruwaito halaccin cin dawãki. Wannan shĩ ne maganar Al- Hasan da Shuraih da 'Aɗa' a da Sa'ĩd bn Jubair. Kuma Shi ne mazhabar shãfi'i da Is'hãƙ. Sun yi hujja da halaccin nãman dawãki da abin da Asmã'u bint Abĩ Bakar Assiddiƙ ta ce, « Mun sõke wata gõɗiya' muka ci a zamanin Manzon Allah,a Madina. » Kuma a cikin Bukhãri da Muslim daga jãbir, Allah Ya yarda da shi, « Mun ci dawãki da jãkunan jẽji a Khaibara, kuma Annabi tsira da aminci sun tabbata a gare shi, ya hana jãkunan gida » Acikin Abĩ Dãwud, « Mun yanke dawãki da alfadarai da jakuna alhãli yunwa ta kãmã mu, amma sai Annabi ya hana mu cin jãkuna da alfadarai, bai hana mu cin dawãki ba » Nĩ, a ganina, ra'ayin cin dawãki ya fi ƙarfi dõmin sũrar ta sauka a Makka, amma hadisin yankan gõɗiyar, a Madĩna aka yi shi. Saboda haka surar ba ta shãfe shi ba. Dũbi Radd Al- Azhãn.