Surah An-Nahl | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 276
Suratul Al-Nahl from 80 to 87
80. Kuma Allah ne Ya sanya muku daga gidajenku wurin natsuwa, kuma Ya sanya muku daga fatun dabbõbin ni'ima wasu gidãje kunã ɗaukar su da sauƙi a rãnar tafiyarku da rãnar zamanku, kuma daga sũfinsu ( 1 ) da gãshinsu da gẽzarsu ( Allah ) Ya sanya muku kãyan ɗãki da na jin dãɗi zuwa ga wani lõƙaci.
81. Kuma Allah ne Ya sanyã muku inuwa daga abin da Ya halitta, kuma Ya sanyã muku ɗãkuna daga duwãtsu, kuma Ya sanyã muku waɗansu riguna ( 2 ) sunã tsare muku zãfi, da waɗansu rĩguna sunã tsare muku makãminku. Kamar wancan ne ( Allah ) Yake cika ni'imarSa a kanku, tsammãnin ku, kuna sallamawa.
82. To, idan sun jũya, to, abin da ya wajaba a kanka, shi ne iyarwã kawai, bayyananniyã.
83. Suna sanin ni'imar Allah, sa'an nan kuma sunã musunta, kuma mafi yawansu kãfirai ne.
84. Kuma a rãnar da Muke tãyar da mai shaida daga kõwace al'umma, sa'an nan kuma bã zã a yi izni ba ga waɗanda suka kãfirta, kuma ba su zama ana nẽman kõmawarsu ba.
85. Kuma idan waɗanda suka yi zãlunci suka ga azãba, sa'an nan bã za a saukake ta daga gare su ba, kuma bã su zama anã yi musu jinkiri ba.
86. Kuma idan waɗanda suka yi shirka suka ga abũbuwan shirkarsu sai su ce: « Yã Ubangijinmu! Waɗannan ne abũbuwanshirkarmu waɗanda muka kasance munã kira baicinKa » . Sai su jẽfamagana zuwa gare su, « Lalle ne ku, haƙĩƙa, maƙaryata ne. »
87. Kuma su shiga nẽman sulhu zuwa ga Allah a rãnar nan, kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa ya ɓace daga gare su.
( 1 ) Sũfi, shi ne gãshin tumãki mai kama da audugã, wabar shi ne gãshin rãƙumi mai laushi, sha'ar, shi ne gãshin awakida gẽzar dawãki. Bai ambaci audugã da kattãni ba, dõmin a wajen shũka suke.
( 2 ) Rĩgã dõmin zãfi da sanyi daga sũfi da wabar da gãshi da audugã da kattãni da rĩga dõmin makãmi shi ne sulke, dõmin makãmi daga baƙin ƙarfe yake kamar takõbi, mãshi da kibiya.