Hausa translation of the meaning Page No 275

Quran in Hausa Language - Page no 275 275

Suratul Al-Nahl from 73 to 79


73. Kuma sunã bautã wa, baicin Allah, abin da yake bã ya mallakar wani arziki dõminsu, daga sammai da ƙasa game da kõme, kuma bã su iyawa ( ga aikata kõme ) .
74. Sa'an nan kada ku bãyar da waɗansu misãlai ga Allah. Lalle ne Allah Yanã sani, kuma kũ, ba ku sani ba.
75. Allah Yã buga wani misali da wani bãwa wanda bã ya iya sãmun ĩko a kan yin kõme, da ( wani bãwa ) wanda Muka azurtã shi daga gare Mu da arziki mai kyau. Sa'an nan shĩ yanã ciyarwa daga arzikin, a asirce da bayyane. Shin sunã daidaita? Gõdiya ta tabbata ga Allah. Ã'a mafi yawansu ba su sani ba.
76. Kuma Allah Ya buga wani misãli, maza biyu, ɗayansu bẽbe ne, ba ya iya sãmun ikon yin kõme, kuma shi nauyi ne a kan mai mallakarsa, inda duk ya fuskantar da shi, bã ya zuwa da wani alhẽri. Shin, yanã daidaita, shi da ( namiji na biyu ) wanda yake umurni da a yi ãdalci kuma yanã a kan tafarki madaidaici?
77. Kuma ga Allah gaibin ( 1 ) sammai da ƙasa yake, kuma al'amarin Sã'a bai zama ba fãce kamar walƙãwar gani, kõ kuwa shĩ ne mafi kusa! Lalle Allah a kan dukan kõme Mai ikon yi ne.
78. Kuma Allah ne Ya fitar da ku daga cikunan iyãyenku, ba da kunã sanin kõme ba, kuma Ya sanya muku ji da gannai da zukãta, tsammãninku zã ku gõde.
79. Shin ba su ga tsuntsãye ( 2 ) ba sunã hõrarru cikin sararin sama bãbu abin da yake riƙe su fãce Allah? Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni.
( 1 ) Ɓõye lõkacin Ƙiyãma a bãyan bayãnin tabbatar aukuwarta yanã daga cikin ni'imõmin Allah, dõmin mai hankali ya yi tattãli sabõda ita.
( 2 ) Tsuntsãye hõrarru a cikin sararin sama, ana nufi da su, a ganĩna, Allah ne Ya san haƙĩƙa, su ne jirãgen sama, sabõda ambaton hõrẽwa tãreda sũ a cikin sararin samãniya, dõmin abin da aka hõre, ana hõronsa ne dõmin a ci amfãninsa a lõkaci da wurin hõron. Tsuntsãyen al'ãda bã su da wani amfãni a gare mu a lõkacin da suke a cikin sãrãrin sama. Sabõda haka bãbu wani abu, sai jirgin sama. Bã zã a ce anã nufin shãho ba a lõkacin farauta, dõmin wannan amfãni yã yi kaɗan bisa ga abin da sũrar take ƙidãyãwa na ni'imõmin Allah a kan mutãne gabã ɗaya. Farauta kẽɓãɓɓiya ce ga mutãnen ƙauye kawai.