Hausa translation of the meaning Page No 286

Quran in Hausa Language - Page no 286 286

Suratul Al-Asra from 39 to 49


39. Wancan yãnã daga abin da Ubangijinka Ya yi wahayi zuwa gare ka na hikima. Kuma kada ka sanya wani abin bautãwa na daban tãre da Allah har a jẽfa ka a cikin Jahannama kanã wanda ake zargi, wanda ake tunkuɗẽwa ( 1 )
40. Shin fa, Ubangijinku Ya zãɓe ku da ɗiya maza ne, kuma Ya riƙi 'ya'ya mãta daga malã'iku? ( 2 ) Lalle ne kũ, haƙĩƙa, kunã faɗar magana mai girma!
41. Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun sarrafa bayãni a cikin wannan Alƙur'ãni dõmin su yi tunãni, kuma bã ya ƙãra musu kõme fãce gudu.
42. Ka ce: « Dã akwai waɗansu abũbuwan bautãwa tãre da shi, kamar yadda suka faɗa, a lõkacin, dã ( abũbuwan bautãwar ) sun nẽmi wata hanya ( 3 ) zuwa ga Ma'abũcin Al'arshi. »
43. TsarkinSa yã tabbata kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke faɗã, ɗaukaka mai girma.
44. Sammai bakwai da ƙasa da wanda yake a cikinsu sunã yi Masa tasbĩhi. Kuma bãbu wani abu fãce yanã tasbĩhi game da gõde Masa, kuma amma ba ku fahimtar tasbĩhinsu. Lalle ne shĩ, Ya kasance Mai haƙuri ne, Mai gãfara.
45. Kuma idan ka karanta Alƙur'ani, ( 4 ) sai Mu sanya a tsakãninka da tsakanin waɗanda bã su yin ĩmãni da Lãhira wani shãmaki mai suturcẽwa.
46. Kuma Mu sanya marufai a kan zukãtansu dõmin kada su fahimce shi, da, wani nauyi a cikin kunnuwansu, kuma idan ka ambaci Ubangijinka, a cikin Alƙur'ãni shĩ kaɗai, sai su jũya a kan bayayyakinsu dõmin gudu.
47. Mũ ne Mafi sani game da abin da suke saurãre da shi a lõkacin da suke yin saurãren zuwa gare ka, kuma a lõkacin da suke mãsu gãnãwa a tsakãninsu a lõkacin da azzãlumai suke cẽwa, « Bã ku biyar kõwa fãce wani namiji sihirtacce. »
48. Ka dũba yadda suka buga maka misãlai, sai suka ɓace bã su iya sãmun hanya.
49. Kuma suka ce: « Shin, idan mun kasance ƙasũsuwa da, niƙaƙƙun gaɓãɓuwa ashe, lalle ne mũ haƙĩƙa, waɗanda ake tãyarwa ne a wata halitta sãbuwa? »
( 1 ) Wannan shĩ ne ƙarshen muƙãrana tsakãnin shiryarwar da Alƙur'ãni ya kãwo wa dũniya da abin da Attaura ta kãwo wa Banĩ Isrã'ĩla. Kuma akwai daidatãwa a cikinsu a tsakãnin hãlãye mãsu kyau da kĩshiyõyinsu, watau hãlãye mãsu mũni.
( 2 ) Farkon muƙãrana a tsakãninal'ãdun mushirikai da shiryarwar Alƙur'ãni dõmin gyãra tunãninsu ga karɓar ĩmãnin tauhĩdi.
( 3 ) Dã su abõkan tãrayyar sun nẽmi hanya zuwa ga Allah dõmin su yãƙe shi sabõda Ya ce Al'arshi Tãsa ce, Shi kaɗai, dõmin su sãmi nãsu rabon, sabõda Al'arshi tã haɗiye kõme, har da su.
( 4 ) Mushirikai jahilai ne, ba su iya ɗaukar jãyayyar magana, sabõda sun fi kusanta zuwa ga dabbõbi ga tunãninsu, bisa gare su zuwa ga mutãne, kõ da yake sauran jikinsu na mutãne ne. Sabõda haka a kõ yaushe sunã kusa ga faɗan tãyar da hankali da dõke- dõke. Sabõda haka Allah Yasanya tsari ga AnnabinSa da wanda ya bi hanyar Annabin,wajen shiryar da mutãne game da karanta Alƙur'ãni. Bã zã su iya fãɗa mai karanta Alƙur'ãni da dũka ba, kuma tsõronsa suke ji dõmin kwarjinin Alƙur'ãni.