Hausa translation of the meaning Page No 287

Quran in Hausa Language - Page no 287 287

Suratul Al-Asra from 50 to 58


50. Ka ce: « Ku kasance duwãtsu ko kuwa baƙin ƙarfe. »
51. « Kõ kuwa wata halitta daga abin da yake da girma a cikin ƙirazanku. » To zã su ce « Wãne ne zai mayar da mu? » Ka ce: « Wanda Ya ƙaga halittarku a fabkon lõkaci. » To, zã su gyaɗa kansu zuwa gare ka, kuma sunã cẽwa, « A yaushene shi? » Ka ce: « Akwai tsammãninsa ya kasance kusa. »
52. « A rãnar da Yake kiran ku, sa'an nan ku riƙa karɓãwa game dã gõde Masa, kuma kunã zaton ba ku zauna ba fãce kaɗan. »
53. Kuma ka cẽ wa bãyiNa, su faɗi kalma ( 1 ) wadda take mafi kyau. Lalle ne Shaiɗan yanã sanya ɓarna a tsakãninsu. Lalle ne Shaiɗan ya kasance ga mutum, maƙiyi bayyananne.
54. Ubangijinku ne Mafi sani game da ku. Idan Ya so, zai yi muku rahama, kõ kuwa idan Yã so zai azabtãku. Kuma ba Mu aika ka kanã wakĩli a kansu ba.
55. Kuma Ubangijinka ne Mafi sani game da wanda yake a cikin sammai da ƙasa. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun fĩfĩta sãshen Annabãwa a kan sãshe kuma Mun bai wa Dãwũda zabũra. ( 2 )
56. Ka ce: « Ku kirãyi waɗanda kuka riya, baicinSa. » To, ba su mallakar kuranyẽwar cũta daga gare ku, kuma haka jũyarwa. « ( 3 ) »
57. Waɗancan, waɗanda suke kiran, ( 4 ) sunã nẽman tsãni zuwa ga Ubangijinsu. Waɗanne ne suke mafĩfĩta a kusanta? Kuma sunã fãtan sãmun rahamarSa, kuma sunã tsõron azãbarSa. Lalle ne azãbar Ubangijinka ta kasance abar tsõro ce.
58. Kuma bãbu wata alƙarya fãce, Mu ne mãsu halaka ta a gabãnin Rãnar Ƙiyãma kõ kuwa Mũ mãsu azãbta ta ne da azãba mai tsanani. Wancan ya kasance a cikin littãfi rubũtacce.
( 1 ) Ka ce wa bãyĩNa, mutãne, idan sunã magana su auna kalmõmin da suke zance da su, sa'an nan su riƙa amfãni da kalma mafi kyãwo dõmin kada shaiɗan ya sãmi mashiga daga maganarsu zuwa ga zukãtansu, ya sanya ɓarna a tsakãninsu.
( 2 ) Muƙãrana a tsakãnin Annabãwa. Allah Yã fĩfĩta waɗansu a kan waɗansu. Falalar Dãwũda a kan waɗansu Annabãwa da zabũra ne to inã fĩfĩkon wanda aka bai wa Alƙur'ãni mafĩfĩcin littafi da sauran Annabãwa?
( 3 ) Bã zã su iya jũyar da cũta daga gare ku zuwa ga wani ko kuwa daga wani zuwa gare ku ba.
( 4 ) Waɗanda kãfirai ke nẽman tawassuli da su zuwa ga Allah, sũ ma sunã nẽman abin da zai sãdar da su zuwa ga Allah, sabõda haka bãbu bambanci a tsakãnin mai tawassuli da wanda ake tawassulin da shi ga kusanta zuwa ga Allah. Bãbu mai kusanta zuwa ga Allah sai da taƙawa ga ibãdarSa kawai.