Hausa translation of the meaning Page No 290

Quran in Hausa Language - Page no 290 290

Suratul Al-Asra from 76 to 86


76. Kuma lalle ne, sun ( 1 ) yi kusa, haƙĩƙa, su tãyar da hankalinka daga ƙasar, dõmin su fitar da kai daga gare ta. Kuma a lõkacin, bã zã su zauna ba a kan sãɓãninka fãce kaɗan.
77. Hanyar waɗanda, haƙĩƙa, Muka aika a gabãninka, daga ManzanninMu, kuma bã zã ka sãmi jũyarwa ba ga hanyarMu.
78. Ka tsayar da salla ( 2 ) a karkatar rãnã zuwa ga duhun dare da lõkacin fitar alfijir lalle ne karãtun fitar alfijir ( 3 ) ya kasance wanda ake halarta.
79. Kuma da dare, sai ka yi hĩra ( 4 ) da shi ( Alƙur'ãni ) akan ƙãri gare ka. Akwai tsammãnin Ubangijinka Ya tãyar da kai a wani matsayi gõdadde.
80. Kuma ka ce: « Yã Ubangijĩna! ( 5 ) Ka shigar, da ni shigar gaskiya, kuma Ka fitar da ni fitar gaskiya. Kuma Ka sanya mini, daga gunKa, wani ƙarfi mai taimako. »
81. Kuma ka ce: « Gaskiya tã zo, kuma ƙarya ta lãlãce. Lalle ne ƙarya ta kasance lãlãtacciya. »
82. Kuma Munã sassaukarwa daga Alƙur'ãni, abin da yake waraka ne da rahama ga mũminai. Kuma bã ya ƙãra wa azzãlumai ( kõme ) fãce hasãra.
83. Kuma idan Muka yi ni'ima a kan mutum, ( 6 ) sai ya hinjire, kuma ya nĩsanta da gefensa, kuma idan sharri ya shãfe shi, sai ya kasance mai yanke ƙauna.
84. Ka ce: « Kõwa ya yi aiki a kan hanyarsa. Sa'an nan Ubangijinka ne Mafi sani ga wanda yake mafi shiryuwa ga hanya. »
85. Sunã tambayar ka ga rũhi. Ka ce: « Rũhi daga al'amarin Ubangijina ne, kuma ba a bã ku ( kõme ) ba daga ilmi fãce kaɗan. »
86. Kuma lalle ne idan Mun so, haƙĩƙa, Munã tafiya da abinda Muka yi wahayi zuwa gare ka. Sa'an nan kuma bã za ka sãmi wani wakĩli ba dõminka game da shi a kanMu.
( 1 ) Muƙãrana a tsakãnin mai aiki dõmin Allah, bã a iya jũyarda shi daga aikinsa dõmin nẽman wata kamãla, amma mai aikin dũniya anã iya canja shi dõmin haka. Kuma bambancin hijira da kõra waɗanda suka kõri Annabinsu sai a halaka su, amma waɗanda Annabinsu ya yi hijira gabãnin azãba, to, bã zã a halaka su ba.
( 2 ) Tsayar da salla a cikin lõkutanta, shi ne yake hana a yaudari mutum da magana har a sanya shi ya yi abin da bai kamãta ba, ko kuma ya yi abin da sharĩ'a ta hana.
( 3 ) Karãtun fitar alfijir, ana nufin sallar asuba. Sabõda haka anã son dõgon karãtu a cikinta, gwargwadon fãrã ta a duhun dare a bayan fitar alfijir.
( 4 ) Hĩra da Alƙur'ãni, watau a yi sallõlin nãfila na dare, shafa'i bibbiyu, a ƙãre da wutri. Ga Annabi tahajjudi da wutrin wãjibi ne ƙãri a kan abin da aka ɗõra wa sauran mutãne, a lõkacin da yake zaune a gida. Ga saura mutãne wutri sunna ce, kamar sallõlin ĩdi da rõkon ruwa da husũfin rãnã da na wata. A nan akwai bambanci a tsakãnin Annabi da jama'arsa a wajen wutri.
( 5 ) Kuma ka yi addu'a a cikin sallakra da bãyanta da wannan addu'a dõmin ta nũna sallamãwarka ga Ubangijinka Allah.
( 6 ) Muƙãrana a tsakãnin hãlãye biyu na mutum, hãlin tsanani da hãlin cũta.