Hausa translation of the meaning Page No 291

Quran in Hausa Language - Page no 291 291

Suratul Al-Asra from 87 to 96


87. Fãce da rahama daga Ubangijinka. Lalle ne falalarSa ta kasance mai girma a kanka.
88. Ka ce: « Lalle ne idan mutãne da aljannu sun tãru a kan su zo da misãlin wannan Alƙur'ãni bã zã su zo da misãlinsa ba, kuma kõ dã sãshinsu yã kasance, mataimaki ga sãshi. »
89. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun caccanza dõmin mutãne, a cikin wannan Alƙur'ãni, daga kõwane misãli sai mafi yawan mutãne suka ƙi ( kõme ) fãce kãfirci,
90. Kuma suka ce: « Bã zã mu yi ĩmãni ba dõminka sai kã ɓuɓɓugar ( 1 ) da idan ruwa daga ƙasa. »
91. « Kõ kuma wata gõna daga dabĩnai da inabi ta kasance a gare ka. Sa'an nan ka ɓuɓɓugar da ƙõramu a tsakãninta ɓuɓɓugarwa. »
92. « Kõ kuwa ka kãyar da sama a kanmu kaɓukka kõ kuwa ka zo da Allah, da malã'iku banga- banga. »
93. « Kõ kuwa wani gida na zĩnãriya ya kasance a gare ka, kõ kuwa ka tãka a cikin sama. Kuma bã zã mu yi ĩmãni ba ga tãkawarka, sai ka sassaukõ da wani littãfi a kanmu, munã karantã shi. » Ka ce: « Tsarki ya tabbata ga Ubangijĩna! Ban kasance ba fãce mutum, Manzo. »
94. Kuma bãbu abin da ya hana mutãne su yi ĩmãni, a lõkacin da shiriya ta jẽ musu, fãce sunce, « Shin, Allah zai aiko mutum ya zamo yana Manzo. »
95. Ka ce: « Dã malã'iku sun kasance a cikin ƙasa, kuma sunã tafiya, sunã masu natsuwa, lalle ne dã mun saukar da malã'ika daga sama ya zama manzo a kansu. »
96. Ka ce: « Allah Yã isa zama shaida a tsakãnina da ku. Lalle Shi Ya kasance ga bãyinsa, mai ƙididdigewa ne Mai gani. »
( 1 ) Kãfiri bã ya iya hangen abinda bã a iya taɓa shi da gaɓoɓin ji na jiki, dõmin haka suka nẽmi ɗayan waɗannan abũbuwa ya auku kãmin su yi ĩmãni. Mũmini yanã kange da ganin basĩra, dõmin haka ya wadãtu da zaman Alƙur'ani ãyã mai isa ga ya yi ĩmãni da shi.