Hausa translation of the meaning Page No 296

Quran in Hausa Language - Page no 296

Suratul Al-Kahf from 21 to 27


21. Kuma kamar wancan ne, Muka nũna su ( gare su ) dõmin su san lalle wa'adin Allah gaskiya ne, kuma lalle ne Sa'a bãbu shakka a cikinta. A lõkacin da suke jãyayyar al'amarinsu a tsakãninsu ( 1 ) sai suka ce: « Ku gina wani gini a kansu, Ubangijinsu ne Mafi sani game da su. » Waɗanda suka rinjãya a kan al'amarinsu suka ce: « Lalle mu riƙi masãllãci a kansu. »
22. Zã su ce: « Uku ne da na huɗunsu karensu. » Kuma sunã cẽwa, « Biyar ne da na shidansu karensu, » a kan jĩfa a cikin duhu. Kuma sunã cẽwa, « Bakwaine da na takwas ɗinsu karensu. » Ka ce: « Ubangijĩna ( 2 ) ne Mafi saniga ƙidãyarsu, bãbu wanda ya san su fãce kaɗan. » Kada ka yi jãyayya bayyananna. Kuma kada ka yi fatawa ( 3 ) ga kõwa daga gare su a cikin al'amarinsu.
23. Kuma kada lalle ka ce ga wani abu, « Lalle ni, mai aikatãwa ne ga wancan a gõbe. »
24. Fãce idan Allah Ya so. Kuma ka ambaci Ubangijinka idan ka manta, kuma ka ce: « Ɗammãni ga Ubangijĩna, Ya shiryar da ni ga abin da yake shi ne mafi kusa ga wannan na shiriya. »
25. Kuma suka zauna a cikin kõgonsu shẽkaru ɗarĩ uku kuma suka daɗa tara.
26. Ka ce: « Allah ne Mafi sani ga abin da suka zauna. Shĩ ne da ( sanin ) gaibin sammai da ƙasa. Mũne ne ya yi ganinSa da jinSa! Bã su da wani majiɓinci baicinSa kuma bã Ya tãrayya da kõwa a cikin hukuncinsa. »
27. Ka karanta abin da aka yi wahayi zuwa gare ka, na littãfin Ubangijinka. Bãbu mai musanyãwa ga kalmõminSa kuma bã zã kã sãmi wata madõgara ba daga waninsa.
( 1 ) Muhãwarar mũminai da kãfirai, da yadda kãfirai ke zartar da al'amari bã da ambaton yardar Allah Ubangijinsu ba. Dayadda suke yin sãri- faɗi ga matsalõlin ilmi da ya kamãta a mayar da saninsu ga Allah.
( 2 ) Bayãnin ladubban magana amatsalõlin ilmi da na aiki. Bãbu wanda ya san gaibu sai Allah. Bã a tambayar mãlaman ɓata da son zũciya, dõmin sãri- faɗi suke yi ga jawãbin mai tambaya.
( 3 ) Dõmin haka ba a yin fatawa a wurin mãlamin bidi'a kõ jãhili dõmin zai faɗi abin da yake so, kõ kuma ya yi ƙaddari faɗi, jĩfa a cikin duhu.