Hausa translation of the meaning Page No 295

Quran in Hausa Language - Page no 295 295

Suratul Al-Kahf from 16 to 20


16. « Kuma idan kun nĩsance su sũ da abin da suke bautãwa,fãce Allah, to, ku tattara zuwa ga kõgon sai Ubangijinku Ya watsa muku daga rahamarSa kuma Ya sauƙaƙe muku madõgara daga al'amarinku. »
17. Kuma kanã ganin rãnã idan ta fito tanã karkata daga kõgonsu wajen dãma kuma idan ta fãɗi tanã gurgura su wajen hagu, kuma su, sunã a cikin wani fili daga gare shi. Wannan abu yanã daga ãyõyin Allah. Wanda Allah Ya shiryar, to shĩ ne mai shiryuwa, kuma wanda Allah Ya ɓatar to bã zã ka sãmar masa wani majiɓinci mai shiryarwa ba.
18. Kuma kanã zaton su farkakku ne, alhãli kuwa sũ mãsu barci ne. Munã jũya su wajen dãma da wajen hagu, kuma karensu yanã shimfiɗe da zirã'õ'in ƙafãfuwansa ga farfãjiya ( ta kõgon ) . Dã ka lẽka ( a kan ) su () lalle ne, ka jũya daga gare su a guje kuma () lalle ne ka cika da tsõro daga gare su.
19. Kuma kamar wannan ne Muka tãyar da su, dõmin ( 1 ) su tambayi jũna a tsakãninsu. Wani mai magana daga cikinsu ya ce: « Mẽne ne lõkacin da kuka zauna? » suka ce: « Mun zauna yini ɗaya ko sãshen yini. » Suka ce: « Ubangijinku ne Mafi sani ga abin da kuka zauna. To, ku aika da ɗayanku, game da azurfarku wannan, zuwa ga birnin. ( 2 ) Sai ya dũba wanne ne mafi tsarki ga abin dafãwa, sai ya zo muku da abinci daga gare shi. Kuma sai ya yi da hankali, kada ya sanar da ku ga wani mutum. »
20. « Lalle ne sũ idan sun kãmã ku, zã su jẽfẽ ku, kõ kuwa su mayar da ku a cikin addininsu kuma bã zã ku sãmi babban rabo, ba, a sa'an nan har abada. »
( 1 ) Mahãwarar muminai a bãyanbarcin shẽkara ɗari uku, amma duk da haka sunã ikin hankalinsu sunã mayar da al'amari ga Allah.
( 2 ) Birnin shi ne Tarasus. Sunan sarƙinsu Daƙayãnus.