Hausa translation of the meaning Page No 299

Quran in Hausa Language - Page no 299 299

Suratul Al-Kahf from 46 to 53


46. Dũkiya da ɗiya, ( 1 ) sũ ne ƙawar rãyuwar dũniya, kuma ayyuka mãsu wanzuwa na ƙwarai sun fi zama alhẽri a wurin Ubangijinka ga lãda kuma sun fi alhẽri ga bũri.
47. Kuma a rãnar da Muke tafiyar da duwãtsu, kuma ka ga ƙasa bayyane, kuma Mu tãra su har ba Mu bar kõwa ba daga gare su.
48. Kuma a gittã ( 2 ) su ga Ubangijinka sunã sahu guda, ( Mu ce musu ) , « Lalle ne haƙĩƙa kun zo Mana, kamar yadda Muka halitta ku a farkon lõkaci. Ã'a, kun riya cẽwa bã zã Mu sanya mukuwani lõkacin haɗuwa ba. »
49. Kuma aka aza littãfin ayyuka, sai ka ga mãsu laifi sunã mãsu jin tsõro daga abin da ke cikinsa, kuma sunã cẽwa « Kaitonmu! Mẽne ne ga wannan littãfi, bã ya barin ƙarama, kuma bã ya barin babba, fãce yã ƙididdige ta? » Kuma suka sãmi abin da suka aikata halarce. Kuma Ubangijinka bã Ya zãluntar kõwa.
50. Kuma a lõkacin da Muka ce wa malãiku, « Ku yi sujada ga Ãdamu. » Sai suka yi sujada fãce Iblĩsa, yã kasance daga aljannu sai ya yi fãsiƙanci ga barin umurnin Ubangijinsa, To fa, ashe, kunã riƙon sa, shi da zũriyarsa, su zama majiɓinta baicin Ni, alhãli kuwa su maƙiya ne a gare ku? Tir da ya zama musanya ga azzãlumai. ( 3 )
51. Ban shaida musu halittar sammai da ƙasa ba, kuma ban ( shaida musu ) halittar rãyukansu ba kuma ban kasance mai riƙon mãsu ɓatarwa ( da wani ) su zama mataimaka ba.
52. Kuma da rãnar da Allah Yake cẽwa, « Ku kirãyi abõkan tarayyãTa, waɗanda kuka riya. » Sai su kirãye su, sai bã zã su karɓa musu ba, kuma Mu sanya Maubiƙa ( 4 ) ( Mahalaka ) a tsakãninsu,
53. Kuma mãsu laifi suka ga wutã suka tabbata lalle ne, sũ mãsu, auka mata ne, kuma ba su sãmi majũya ba daga gare ta.
( 1 ) Dũkiya da ɗiya, ƙawar dũniya ne, idan suka zama abin a1fahari ga mai su, amma idan an ciyar da dũkiya ga tafarkin Allah, kuma aka karantar da ɗiya ga bisa tafarkin hanyar sharĩ'a suka tãshi Musulmin ƙwarai, to, sun zama aikin sharĩ'a na Lãhira kẽ nan.
( 2 ) Bayãnin abũbuwan da ke aukuwa a wurin hisãbi ke nan gamãsu bin son zũciya, su bar sharĩ'a.
( 3 ) Allah Shĩ ne Ya halitta mutãne, kuma Ya ɗaukaka darajarsu, dõmin Yã sanya malã'iku su yi sujada ga ubansu Ãdamu. Sabõda wannan sõyayyar kuma Ya bã su sharĩ'ar da zã su bi su shiryu har su shiga Aljanna, amma sai suka ƙi, suka kõma wa Shaiɗanwanda yake shi ne farko maƙiyin ubansu, Ãdamu, wanda ya ƙi yi wa sujada, har aka la'ane shi, sunã bin sa, shi da ɗiyansa, alhãli kuwa bãbu wani abin da zã su iya yimusu na alhẽri ko na sharri, dõmin sũ ma halitta ne kamarsu. Bã su san kõme ba a sama kõ a ƙasa, kuma Allah bã Ya yin ma'amalar kõme da su. Wanda ya bi Shaiɗan ya bar Allah, to, yã yi mugunyar musanya, kuma yã zãlunci kansa ƙwarai.
( 4 ) Maubiƙã sũnan wani rãfi ne na wuta, asalinsa daga 'Wabiƙa,' wãtau yã halaka. Za a sanya wannan rãfi a tsakãnin mãsu bin Shaiɗan da sũrõringumãka, da wanda ya shirya musu gumãkan, sunã bauta musu.