Hausa translation of the meaning Page No 300

Quran in Hausa Language - Page no 300 300

Suratul Al-Kahf from 54 to 61


> 54. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun jujjũya, a cikin wannan Alƙur'ãni, daga kõwane irin misãli ga mutãne ( dõmin su gãne, su bi sharĩ'a ) , kuma mutum yã kasance mafi yawan abu ga jidãli. ( 1 )
55. Kuma bãbu abin da ya hana mutãne su yi ĩmãni a lõkacinda shiriya ta zo musu, kuma su nẽmi gãfara daga Ubangijinsu, fãce hanyar farko ( 2 ) ta je musu kõ kuma azãba ta jẽ musu nau'i- nau'i.
56. Kuma ba Mu aika Manzanni ba fãce sunã mãsu bãyar da bushãra kuma mãsu gargaɗi, kuma waɗanda suka kãfirta sunã jidãli da ƙarya dõmin su ɓãta gaskiya da ita, kuma suka riƙi ãyõyiNa da abin da aka yi musu gargaɗi da shi abin izgili.
57. Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda aka tunãtar game da ãyõyin Ubangijinsa, sai ya bijire daga barinsu, kuma ya manta abin da hannãyensa suka gabãtar? Lalle ne Mũ, Mun sanya abũbuwan rufi a kan zukãtansu dõmin kada su fahimcẽ shi, kuma a cikin kunnuwansu ( Mun sanya ) wani nauyi, kuma idan kã kĩrayẽ su zuwa ga shiriya, to, bã zã su shiryu ba, a sa'an nan, har abada.
58. Kuma Ubangijinka Mai gãfara ne, Ma'abũcin rahama. Dã Yanã kãma su sabõda abin da suka sanã'anta, lalle ne, dã Ya gaggauta azãba a gare su. Ã'a, sunã da lõkacin alkawari, ( wanda ) bã zã su sãmi wata makõma ba, baicinSa. ( 3 )
59. Kuma waɗancan alƙaryu ( 4 ) Mun halaka su, a lõkacin da suka yi zãlunci, kuma Muka sanya lõkacin alkawarin, ga halaka ( 5 ) su.
60. Kuma a lõkacin da Mũsã ( 6 ) ya ce wa yãronsa, « Bã zan gushe ba sai na isa mahaɗar tẽku biyu, kõ in shũɗe da tafiya shekara da shẽkaru. »
61. To, a lõkacin da suka isa mahaɗar tsakãninsu sai suka manta kĩfinsu, sai ya kãma tafarkinsa a cikin tẽku kamar bĩga.
( 1 ) Jidãli, shĩ ne jãyayya, alhãli kuwa mutum yã san yanã kanƙarya.
( 2 ) Hanyar farko ita ce Allah Ya halaka su sabõda laifinsu kõ kuma azãba ta jẽ musu nau'i- nau'i, dõmin su musulunta sai ƙarshe idan sun ƙi a halaka su. Waɗansu sun fassara 'ƙubala' ko 'ƙibala' da ta fuskance su bayyane, bisa ga karãtun kalmar 'ƙibala' da wasalin ƙasa, da ma'anar azaba.
( 3 ) Watau ba su da wata makõma su bar wannan lõkacin alkawarin saukar azãbar.
( 4 ) Alƙaryun Ãdãwa da samũdãwa da waɗansunsu.
( 5 ) Kõme Allah Zai yi, sai Yã sanya masa lõkacin aukuwarsa, kuma bã zai aukun ba sai ajalin nan da Ya ambata masa ya zo.
( 6 ) Shĩ ne MũSã bn Imrãn Manzon Banĩ Isrã'ĩla. Sababin wannan ƙissa, an tambaye shi ne, « Wãne ne ya fi ilmi a saninsa? » Sai ya ce: « Shĩ ne ya fi. Wannan jawãbi nãsa gaskiya ne, dõmin shĩ ne Manzon zãmaninsa, shĩ ne aka bai wa Attaura, kuma Allah Ya yi magana da shi, sai dai ya mance bai ce Allah Ya fi sani ba, dõmin haka aka ce masa ya tafi neman ilmi ga wani mutum a magamar tẽku biyu. Wannan bãwan Allah Haliru ne. Yãron Mũsã kuwa, shĩ ne Yũsha'u bnNũn, Manzon Allah a bãyan Mũsã.Kĩfin kuma na guzurinsu ne wanda Allah Ya umurce shi ya ɗauka, sõyayye, kuma aka ce musu duka inda yai rai, to, a nan ne Bãwan Allahyake, mai shirin ƙãra wa Mũsã ilmi. Mayar da ilmi ga Allah, shĩ ne ladabin shari'a.»