Hausa translation of the meaning Page No 313

Quran in Hausa Language - Page no 313 313

Suratul Ta-Ha from 13 to 37


13. « Kuma Nĩ Nã zãɓe ka. Sai ka saurãra ga abin da ake yin wahayi. »
14. « Lalle, Nĩ Ni ne Allah. Bãbu abin bautawa fãce Ni. Sai ka bauta Mini, kuma ka tsayar da salla dõmin tuna Ni. »
15. « Lalle ne Sa'a mai zuwa ce, lnã kusa da In ɓõye ta dõmin a sãka wa dukan rai da abin da yake aikatãwa. »
16. « Sabõda haka, kada wanda bã ya yin ĩmãni da ita kumaya bi son zuciyarsa, ya taushe ka daga gare ta har ka halaka. »
17. « Kuma wãce ce waccan ga dãmanka yã Mũsa! »
18. Ya ce: « Ita sandãta ce, inã dõgara a kanta, kuma inã kakkaɓar ganye da ita a kan ƙananan bisãshẽna kuma inã da waɗansu bukãtõci ( 1 ) na dabam a gare ta. »
19. Ya ce: « Ka yi jĩfa da ĩta, yã Mũsã! »
20. Sai ya jẽfa ta. Sai gã ta dabbar macĩjiya, tanã tafiya da gaggãwa.
21. Ya ce: « Ka kãma ta kuma kada ka ji tsõro. Za Mu mayar da ita ga hãlinta na farko. »
22. « Kuma ka haɗa hannunka zuwa ga damtsenka, ya fita yanã fari, bãbu sõfane, wata ãyã ta dabam. »
23. « Dõmin Mu nũna maka daga ãyõyinMu manya. »
24. « Ka tafi zuwa ga Fĩr'auna. Lalle shĩ ya ƙẽtare haddi ( da girman kai ) . »
25. Ya ce: « Ya Ubangiji! Ka buɗa ( 2 ) mini, ƙirjĩna. »
26. « Kuma ka sauƙaƙe mini al'amarĩna. »
27. « Kuma Ka warware mini wani ƙulli daga harshẽna. »
28. « Su fahimci maganãta. »
29. « Kuma Ka sanya mini wani mataimaki daga mutãnena. »
30. « Hãrũna ɗan'uwana. »
31. « Ka ƙarfafa halittata da shi. »
32. « Kuma Ka shigar da shi a cikin al'amarina. »
33. « Dõmin mu tsarkake Ka da yawa. »
34. « Kuma mu tuna Ka da yawa. »
35. « Lalle Kai, Ka kasance Mai gani gare mu. »
36. Ya ce: « Lalle ne, an bã ka rõƙonka, yã Mũsã! »
37. « Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun yi wata baiwa gare ka a wani lõkacin na dabam. »
( 1 ) Amfãnõnin sanda: Anã riƙonalkĩbla a cikin daji ta zama sitra, anã dõgara a kanta sabõda gajiya kõ rauni. Lĩmãmin Juma'a na dõgara a kanta a lõkacin huɗuba anã fita da ita a cikin ruwan sama anã dõgara a kanta, anã dũkan iyãli da ita dõmin ladabtarwa. A cikin wani Hadĩsi Annabi ya ce: « Ka rãtaye sandarka indaiyãlinka suke ganin ta. » Riƙon sanda na sanya farkawa gabarin dũniya, watau mai ita ya zama a cikin hãlin tafiya.
( 2 ) Ma'anar buɗa ƙirji, shine a sanya masa haƙuri. « »