Hausa translation of the meaning Page No 312

Quran in Hausa Language - Page no 312 312

Suratul Maryam from 96 to 12


96. Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, Mai rahama zai sanya musu so. ( 1 )
97. Sa'an nan Ibin sani kawai Mun sauƙaƙar da shi ( Alƙur'ãni ) a harshenka, dõmin ka yi bushãra da shi ga mãsu aiki da taƙawa kuma ka yi gargaɗi da shi ga mutãne mãsu tsananin husũma.
98. Kuma da yawa Muka halakar da mutãnen ƙarnõni a gabãninsu. Shin kanã jin mõtsin wani guda daga gare su, kõ kuwa kanã jin wata ɗuriya tãsu?
Sũratu Ɗ.H.
Tanã karantar da cẽwa Alƙur’ãni kõ Musulunci, abu ne mai sauƙi dõmin shiryar da mutãne zuwa ga sauƙi, bãbu wahala a cikinsa.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ɗ. H.
2. Ba Mu saukar da Alƙur'ãni a gare ka dõmin ka wahala ba.
3. Fãce dõmin tunãtarwa ga wanda ke tsõron Allah.
4. ( An saukar da shi ) saukarwa daga wanda Ya halitta ƙasa da sammai maɗaukaka.
5. Mai rahama, Ya daidaita ( 2 ) a kan Al'arshi.
6. Abin da yake a cikin sammai nãSa ne, da abin da yake a cikin ƙasa da abin da yake a tsakãninsu da abin da ke ƙarƙashin turɓãya.
7. Kuma idan ka bayyana da magana, to, lalle Shi, Yanã sanin asĩri da mafi bõyuwa.
8. Allah bãbu abin bautãwa fãce Shi. Yanã da sunãye mafiya kyau.
9. Kuma shin, lãbarin Mũsã yãje maka?
10. A lõkacin da ya ga wata wuta, sai ya ce wa iyãlinsa, « Ku dãkata. Lalle ne nĩ, na tsinkãyi wata wuta tsammãnĩna in zo mukuda makãmashi daga gare ta, kõ kuwa in sãmi wata shiriya a kan wutar. »
11. Sa'an nan a lõkacin da ya je mata, aka kira shi, « Ya Mũsã! »
12. « Lalle ne, Nĩ ne Ubangijnka, sai ka ɗẽbe takalmanka ( 3 ) Lalle ne kanã a rãfin nan abin tsarkakẽwa, Ɗuwa. »
( 1 ) Wanda ya bi Allah da gaskiya, Allah zai sanya zukãtan mutãne su sõ shi kamar yadda yake a cikin Hadisi wanda Imãm Tirmizi ya ruwaito daga sa'ad da Abu Huraira.
( 2 ) Allah Ya daidaitu a kan Al'arshi daidaita wadda ta dãce da shi.
( 3 ) An ce wa Mũsã ya ɗẽbe takalmansa dõmin sunã da najasa kõ kuwa sũ kansu najasa ne dõmin ya shiga wuri mai tsarki wanda ake kira Ɗuwa a cikin sahãrar Sina'i a tsakãnin Masar da Madyana. « »