Hausa translation of the meaning Page No 315

Quran in Hausa Language - Page no 315 315

Suratul Ta-Ha from 52 to 64


52. Ya ce: « Saninsu yanã a wurin Ubangijĩna, Ubangijĩna bã Ya ɓacẽwa kuma bã Ya mantuwa. »
53. « Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, kuma Ya shigar muku da hanyõyi a cikinta, kuma Ya saukar da ruwa daga sama. » Sa'an nan game da shi ( 1 ) Muka fitar da nau'i- nau'i daga tsirũruwa dabam- dabam.
54. Ku ci kuma ku yi kiwon dabbõbin ni'imarku. Lalle ne, a cikin wannan akwai ãyõyi ga masu hankali.
55. Daga gare ta ( 2 ) Muka halitta ku, kuma a cikinta Muke mayar da ku, kuma daga gare ta Muke fitar da ku a wani lõkaci na dabam.
56. Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun nũna masa ãyõyinMu dukansu sai ya ƙaryata, kuma ya ƙiya!
57. Ya ce: « Shin kã zo mana ne dõmin ka fitar da mu daga ƙasarmu game da sihirinka, yã Mũsã? »
58. « To, lalle ne munã zo maka da wani sihiri irinsa. Sai ka sanya wani wa'adi a tsakãninmu da tsakãninka bã mu sãɓa masa mũ kai kuma, bã ka sãɓãwa, a wani wuri mai dãcẽwa. »
59. Ya ce: « Wa'adinku shi ne rãnar ƙawa kuma a tãra mutãne da hantsi. »
60. Sai Fir'auna ya jũya, sa'an nan ya tãra mugunyar dabãrarsa, sa'an nan kuma ya zo.
61. Mũsã ya ce musu, « Kaitõnku! Kada ku ƙirƙira ƙarya ga Allah har Ya tumɓuke ku da wata azãba. Kuma wanda ya ƙirƙira ƙarya, yã tãɓe. »
62. Sai suka yi jãyayya ga al'amarinsu a tsakãninsu kuma suka asirta gãnawa.
63. Suka ce: « Lalle ne waɗannan biyun, haƙĩƙa masihirta ne sunã nufin su fitar da ku daga ƙasarku ( 3 ) game da sihirinsu kuma su tafi da tabĩ'arku mafĩficiya. »
64. « Sai ku haɗa dabãrarku sa'an nan kuma ku tafi a sahu guda, kuma haƙĩƙa, wanda ya rinjãya, a yau, ya rabbanta. »
( 1 ) Ruwan.
( 2 ) Ƙasa.
( 3 ) Ya fara da siyãsa dõmin ya karkatar da hankalin mutãne daga ãyõyin Allah. Cewarsa yãyi nufin ya fitar da ku daga ƙasarku, shĩ ne siyãsa dõmin idan mutãne suka ji maganar fitarwa daga ƙasa, sai su manta da kõwace irin magana tawani alhẽri.