Hausa translation of the meaning Page No 333

Quran in Hausa Language - Page no 333 333

Suratul Al-Hajj from 6 to 15


6. Wancan ne dõmin lalle Allah Shi ne Gaskiya, kuma lalle ne shi Yake rãyar da matattu, kuma lalle Shi Mai ikon yi ne a kan kõme.
7. Kuma lalle ne Sa'ar Tãshin Ƙiyãma mai zuwa ce, bãbu shakka a cikinta kuma lalle ne Allah Yanã tãyar da waɗanda suke a cikin ƙaburbura.
8. Kuma daga mutãne akwai mai yin musu ( 1 ) ga Allah bã da wani ilmi ba kuma bã da wata shiriya ba, kuma bã da wani littãfi mai haskakãwa ba.
9. Yanã mai karkatar da sãshensa dõmin ya ɓatar ( da wasu ) daga tafarkin Allah! Yanã da wani wulãkanci a dũniya, kuma Munã ɗanɗana masa azãbar gõbara a Rãnar Ƙiyãma.
10. ( A ce masa ) : « Wancan azaba sabõda abin da hannayenka biyu suka gabatar ne, kuma lalle ne Allah bai zama Mai zãlunci ga bãyinSa ba. »
11. Kuma daga mutãne akwai mai bauta ( 2 ) wa Allah a kan wani gefe. Sa'an nan idan wani alhẽri ya sãme shi, sai ya natsu da shi, kuma idan wata fitina ta sãme shi, sai ya jũya bãya a kan fuskarsa. Yã yi hasãrar dũniya da Lãhira. Waccan ita ce hasãra bayyananna.
12. Yanã kiran baicin Allah, abin da bã ya cũtarsa da abin da bã ya amfãninsa! waccan ita ce ɓata mai nĩsa.
13. Yanã kiran wanda yake lalle cũtarwarsa ce mafi kusa daga amfãninsa! Lalle ne, tir da shi ya zama majiɓinci, kuma tir da ya zama abõkin zama!
14. Lalle ne Allah Yanã shigar da waɗanda suka yi ĩmãni ( 3 ) kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a cikin gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu. Lalle ne Allah Yanã aikata abin da Yake nufi.
15. Wanda ya kasance yanã zaton cẽwa Allah bã zai taimake shi ( 4 ) ba a cikin dũniya da Lãhira to sai ya mĩƙa wata igiya zuwa sama, sa'an nan kuma ya yanke ta, sa'an nan ya dũba. Shin, ko lalle kaidinsa zai gusar da abin da yake ji na takaici?
( 1 ) Kashi na biyu shi ne mũgun malami ko Shaiɗan mai ƙõƙarin ɓatar da mabiyansa wãwãye.
( 2 ) Kashi na uku shi ne munãfuki mai shiga addĩni da biyu.
( 3 ) Kashi na huɗu sũ ne mũminai waɗanda suke tsõron Allah, su tsaya a inda Yatsayar da su. Su ne mafi ƙarancin kashi ga uku na farko.
( 4 ) Wanda yake zaton Allah bã zai taimaki Annabinsa ba kuma yanã jin hushin Allah Ya zãɓi Muhammadu da Annabci, to, sai ya mutu da hushinsa,kuma ya yi dukan kaidin da yake so ya yi, Allah bã zai fãsa abin da Ya yi nufi ba a game da Annabinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.