Hausa translation of the meaning Page No 341

Quran in Hausa Language - Page no 341 341

Suratul Al-Hajj from 73 to 78


73. « Ya ku mutãne! An buga wani misãli, sai ku saurãra zuwa gare shi. Lalle ne waɗanda kuke kira baicin Allah, bã zã su halitta ƙudã ba, kõ da sun tãru gare shi, kuma idan ƙudãn ya ƙwãce musu wani abu, bã zã su kuɓutar da shi ba daga gare shi. Mai nẽma da wanda ake nẽman gare shi sun raunana. »
74. Ba su ƙaddara wa Allah hakkin girmanSa ba. Lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai ƙarfi ne, Mabuwãyi.
75. Allah nã zãɓen Manzanni daga malã'iku kuma daga mutãne. ( 1 ) Lalle Allah, Mai ji ne, Mai gani.
76. Yanã sanin abin da ke gaba gare su da abin da ke bãyansu, kuma zuwa ga Allah ake mayar da al'amura.
77. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi rukũ'i, kuma ku yi sujada, kuma ku bauta wa Ubangijinku, kuma ku aikata alhẽri, tsammãninku, ku sami babban rabo.
78. Kuma ku yi jihãdi a cikin ( al'amarin ) Allah, hakkin JihãdinSa. shĩ ne Ya zãɓe ku alhãli kuwa bai sanya wani ƙunci ( 2 ) ba a kanku a cikin addĩni. Bisa ƙudurcẽwar ubanku Ibrãhĩm, shĩ ne ya yi muku sũna Musulmi ( 3 ) daga gabãnin haka. Kuma a cikin wannan ( Littãfi ya yi muku sũna Musulmi ) , dõmin Manzo ya kasance mai shaida a kanku, kũ kuma ku kasancemãsu shaida a kan mutãne. Sabõda haka ku tsayar da salla kuma ku bãyar da zakka kuma ku amince da Allah, Shi ne Majiɓincinku. Sãbõda haka mãdalla da Shi Ya zama Majiɓinci, mãdalla da Shi ya zama Mai taimako.
( 1 ) Allah nã zaɓen Manzanni daga mutãne da malã'iku kawai. Sabõ da haka bãbu wani manzo da jinsin aljannu kõ wani jinsi, kuma ãyar Sũratul Ahzãb ta 40 tã nũna zãɓen nan ya ƙãre daga Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Duk wanda ya yi da'awar Allah Ya bã shi wani hukumci a bãyan Annabi Muhammadu, kõ dã bai yi da'awar annabci ba, to, shĩ Dajjal ne, bã a bin sa.
( 2 ) Bãbu ƙunci a cikin Musulunci, duk inda aka faɗi tsanani kuma an faɗi yadda sauƙi zai sãmu a kõwane hãli.
( 3 ) Sharaɗin Musulunci ya zama a kan aƙĩdar Ibrãhĩm wanda ya yi wa wannan al'umma sũna da Musulmi tun a zãmaninsa, kuma an ambaci wannan magana a cikin wannan Littafi, wãtau Alƙur'ãni, a cikin sũrar Baƙara ãyã ta 128.