Hausa translation of the meaning Page No 342

Quran in Hausa Language - Page no 342 342

Suratul Al-Mu'minun from 1 to 17


Sũratul Mũminũn
Tanã karantar da haƙĩƙanin ĩmãni da ayyukan ĩmãni. ĩmãni ba ya cika sai da aiki.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Lalle ne, Mũminai ( 1 ) sun sãmi babban rabõ.
2. Waɗanda suke a cikin sallarsu mãsu tawãli'u ne.
3. Kuma waɗanda suke, sũdaga barin yasassar magana, mãsu kau da kai ne.
4. Kuma waɗanda suke ga zakka mãsu aikatãwa ne.
5. Kuma waɗanda suke ga farjõjinsu mãsu tsarẽwa ne.
6. Fãce a kan mãtan aurensu, kõ kuwa abin da hannayen dãmansu suka mallaka to lalle sũ bã waɗanda ake zargi, ba, ne.
7. Sabõda haka wanda ya nẽmi abin da ke bãyan wancan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙẽtarẽwar haddi.
8. Kuma waɗanda suke, sũga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne.
9. Kuma da waɗanda suke, sũ a kan sallõlinsu sunã tsarẽwa.
10. Waɗannan, sũ ne magãda.
11. Waɗanda suke gãdõn ( Aljannar ) Firdausi, ( 2 ) su a cikinta madawwama ne.
12. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta mutum daga wani tsantsa daga lãka.
13. Sa'an nan kuma Muka sanya shi, ɗigon maniyyi a cikin matabbata natsattsiya.
14. Sa'an nan kuma Muka halitta shi gudan jini, sa'an nan Muka halitta gudan jinin tsõka, sa'an nan Muka halitta tsõkar ta zama ƙasũsuwa, sa'an nan Muka tufãtar da ƙasũsuwan da wani nãma sa'an nan kuma Muka ƙãga shi wata halitta dabam. Sabõda haka albarkun Allah sun bayyana, Shi ne Mafi kyaun mãsu halittawa.
15. Sa'an nan kuma ku, bãyan wannan, lalle ne masu mutuwa ne.
16. Sa'an nan kuma lalle ne kũ a Rãnar Ƙiyãma, za a iãyar da ku,
17. Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta, a samanku, hanyõyi bakwai, kuma ba Mu kasance, daga barin halittar, Mãsu shagala ba.
( 1 ) Mũminai su ne waɗanda suke da siffõfin da aka jeranta a cikin ãyõyĩn da ke biye daga ta 2 zuwa ga ta 9.
( 2 ) Asalin firdausi fadama mai ruwa da itãce da ni'ima. Aljannar firdausi ita ce mafi ɗaukakar Aljanna.