Hausa translation of the meaning Page No 353

Quran in Hausa Language - Page no 353 353

Suratul Al-Nur from 28 to 31


28. To, idan ba ku sãmi kõwa a cikinsu ba, to, kada ku shige su, sai an yi muku izni. Kuma idan an ce muku, « Ku kõma. » Sai ku kõma, shi ne mafi tsarkaka a gare ku. Kuma Allah game da abin da kuke aikatãwa, Masani ne.
29. Bãbu laifi a kanku, ga ku shiga gidãje waɗanda bã zaunannu ba, a cikinsu akwai waɗansu kãya nãku. Kuma Allah Yanã sanin abin da kuke nũnãwa, da abin dakuke ɓãyẽwa.
30. Ka ce wa mũminai maza su runtse daga ganinsu, kuma su tsare farjõjinsu. ( 1 ) wannan shĩ ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah, Mai ƙididdigewa ne ga abin da suke sanã'antãwa.
31. Kuma ka ce wa mũminai mãta su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjõjinsu kuma kada su bayyana ƙawarsu fãce abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su dõka da mayãfansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nũna ƙawarsu fãce ga mazansu ko ubanninsu ko ubannin mazansu, ko ɗiyansu, ko ɗiyan mazansu, ko 'yan'uwansu, ko ɗiyan 'yan'uwansu mãtã, kõ mãtan ( 2 ) ƙungiyarsu, ko abin da hannãyensu na dãma suka mallaka, ko mabiya wasun mãsu bukãtar mãta daga maza, kõ jãrirai waɗanda. bã su tsinkãya a kan al'aurar mãtã. Kuma kada su yi dũka da ƙafãfunsu dõmin a san abin da suke ɓõyẽwa daga ƙawarsu.Kuma ku tũba zuwa ga Allah gabã ɗaya, yã ku mũminai! Tsammãninku, ku sãmi babban rabo.
( 1 ) Hukuncin tsare idãnu da rũfe al'aura ga maza da mãtã.
( 2 ) Mãtansu, watau mãtã Musulmi banda mãtã kãfirai, bã ya halatta ga mace kãfira ta ga al'aurar mace Musulma. Mabiya sũ ne mãsu nẽman bukãta ga mãtã wãtau miskĩnai, tsõfaffidaga maza. Al'aurar mace, ɗiya a cikin salla kõ a tãre da wani namiji ajnabi, to, dukan jikinta ne sai fuska da tãfuna, haka kuma a cikin salla. Amma a tãre da mace Musulma tsakãnin cĩbiya da guiwõyi, shi ne al'aura, kuma tãre da muharraminta, dukan abin da bã sasanni ba. Baiwa kamar namiji take, al'aurarsu abin da ke tsakãnin cĩbĩya da guiwa.