Hausa translation of the meaning Page No 352

Quran in Hausa Language - Page no 352 352

Suratul Al-Nur from 21 to 27


21. Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni, kada ku bi hanyõyin Shaiɗan. Kuma wanda ke bin hanyõyin Shaiɗan, to, lalle ne shi, yanã umurni da yin alfãsha da abin da ba a sani ba, kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa, bãbu wani mutum daga gare ku da zai tsarkaka har abada, kuma amma Allah Yanã tsarkake wanda Yake so kuma Allah Mai ji ne, Masani.
22. Kuma kada ( 1 ) ma'abũta falala daga gare ku da mawadãta su rantse ga rashin su bãyar da alhẽri ga ma'abũta zumunta da miskĩnai da muhãjirai, a cikin hanyar Allah. Kuma su yãfe, kuma su kau da kai. shin, bã ku son Allah Ya gãfarta muku, alhãli Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai?
23. Lalle ne waɗannan da suke jĩfar mãtã mãsu kãmun kai gãfilai ( 2 ) mũminai, an la'ane su, a cikin dũniya da Lãhira, kuma sunãda azãba mai girma.
24. A rãnar da harsunansu da hannãyensu, da ƙafãfunsu suke bãyar da shaida a kansu, game da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
25. a rãnar dl Allah Yake cika musu sakamakonsu tabbatacce kuma sunã sanin ( cẽwa ) lalle Allah, Shi ne Gaskiya bayyananna.
26. Miyãgun mãtã dõmin miyagun ( 3 ) maza suke, kuma miyãgun maza dõmin miyãgun mãtã suke kuma tsarkãkan mãtã dõmin tsarkãkan maza suke kuma tsarkãkan maza dõmin tsarkãkan mãtã suke. waɗancan sũ ne waɗanda ake barrantãwa daga abin da ( mãsu ƙazafi ) suke faɗa kuma sunã da gãfara da arziki na karimci.
27. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku shiga gidãje waɗanda bã gidãjenku ba sai kun sãmi izni, kuma kun yi sallama ( 4 ) a kan ma'abũtansu. Wannan ne mafi alhẽri gare ku, tsammaninku, zã ku tuna.
( 1 ) Mai yin alhẽri dõmin Allah kada ya yanke shi daga wanda yake yi wa alhẽrin nan, sabõda yã yi masa wani laifi, da ya shãfe shi ga mutuncinsa kõ dũkiyarsa. Sai ya yãfe, ya kau da kai, ya ci gaba da alhẽrinsa dõmin Allah, kamar yadda Mistahu, wanda yake a cikin dangin Abũbakar As- siddiƙ ya shiga a cikin Hadĩsil Ifk alhãli kuwa Abũbakar ke ciyar da shi sabõda shi misĩkini ne da zumuntã kuma a tsakãninsu, sai Abũbakar ya gãfartamasa, kuma ya ci gaba da bã shi abin da yake bã shi. Haka sauran wuɗanda suka fãda a cikin wannan masifa, an yãfe musu a bãyan an yi musu haddinƙazafi, sai dai wanda ya ɗauki mai girmansa, wãtau Ibn Ubayyu, shi kam ba a yi masa haddi ba dõmin Allah Ya yi masa alkawarin azãba mai tsanani a Lãhira. Watau Musulmi ake yi wa haddi dõmin ya tsarkaka.
( 2 ) Gãfila, ita ce wadda ba ta jarrabi kõme ba sabõda ƙurucciya.
( 3 ) Haka miyãgun kalmõmi bã su dãcẽwa sai daga mũgun mutum. Kuma kalmõmin ƙwaraiba su fitõwa sai daga mutãnen ƙwarai.
( 4 ) Hukuncin shiga gidãje da nẽman izni da sallama.