Hausa translation of the meaning Page No 390

Quran in Hausa Language - Page no 390 390

Suratul Al-Qasas from 36 to 43


36. To, a lõkacin da Mũsã ya jẽ musu da ãyõyinMu bayyanannu, suka ce: « Wannan ba kõme ba sai sihiri, wanda aka ƙãga, kuma ba mu ji wannan ba daga wajen ubanninmu na farko. »
37. Kuma Mũsã ya ce: « Ubangijĩna ne Mafi sanin wanda ya zo da shiriya daga gare Shi, da wanda ãƙibar gida take kasancẽwa agare shi. Lalle ne mãsu zãlunci bã su cin nasara. »
38. Kuma Fir'auna ya ce: « Yã ku mashãwarta! Ban san kunã da wani abin bautãwa baicina ba, sabõda haka ka hũra mini wuta, ya Hãmãnu! a kan lãka ( 1 ) ( dõmin a yi tũbali ) , sa'an nan ka sanya mini bẽne tsammãnĩna zan ninƙãya zuwa ga Ubangijin Mũsã kuma lalle ne ni, haƙĩƙa, inã zaton sa daga maƙaryata. »
39. Kuma ya kangare, shi da rundunõninsa a cikin ƙasa, bã da haƙƙi ba kuma suka zaci cẽwa sũ, bã zã a mayar da su zuwa gare Mu ba.
40. Sai Muka kãma shi, shĩ da rundunõninsa sai Muka jẽfa su a cikin kõgi. Sai ka dũbi yaddaãƙibar azzãlumai ta kasance.
41. Kuma Muka sanya su shũgabanni, sunã kira zuwa ga wuta,kuma a Rãnar Ƙiyãma bã zã a taimake su ba.
42. Kuma Muka biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyakuma a Rãnar Ƙiyãma sunã daga waɗanda aka mũnana halittarsu.
43. Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã Littãfi daga bãyan Mun halakar da ƙarnõnin farko, dõmin su zama abũbuwan kula ga mutãne, da shiriya da rahama, tsammãninsu sunã tunãwa.
( 1 ) Fir'auna ya fãra yin gasasshen tũbali da ake cẽwa ajurru, aka gina masa dõgon bẽne, ya hau samansa, ya harba kibiya ta tafi ama, ta kõmo da jini. Saĩ ya ce: « yã kashe Ubangijin Mũsa. » Bayan haka sai bẽnen ya karye guntu uku' guntu ɗaya ya fãɗa wa sõjansa, da yawa daga cikinsu suka mutu, guntu ɗaya kuma ya fãɗa a cikin ruwa, sauran guntu ɗaya ya fãɗa wa magina, suka mutu. Kuma cẽwar Fir'auna, « Lalle ne nĩ, inã zuton Mũsã daga maƙaryata, » ya nũna girman kansa kawai ne ya hana shi ĩmãni, ba rashin gãnẽwa ba, sai dai kuma sun ga kamar bãbu Tãshin Ƙiyãma.