Hausa translation of the meaning Page No 391

Quran in Hausa Language - Page no 391 391

Suratul Al-Qasas from 44 to 50


44. Kuma ba ka kasance ba ga gẽfen rãfi na yamma a lõkacin da Muka hukunta al'amaru zuwa ga Mũsã, kuma ba ka kasance daga halartattu ba.
45. Kuma amma Mũ, Mun ƙãga halittawar wasu ƙarnõni har lõkatan rãyuwa suka yi tsawo a kansu. Kuma ba ka kasance mazauni ba a cikin mutãnen Madyana, kanã karanta musu ãyõyinMu, amma Mũ Mun kasãnce mãsu aikãwa ( da kai game ( 1 ) da waɗancan lãbarai ) .
46. Kuma ba ka kasance ga gẽfen dũtse ba a lõkacin da Muka yi kira, kuma amma dõmin rahama daga Ubangijinka, dõmin ka yi gargaɗi ga mutãne waɗanda suke wani mai gargaɗi a gabãninka bai je musu ba, tsammãninsu sunã tunãwa.
47. Kuma bã dõmin wata masĩfa ta sãme su ba sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, su ce: « Yã Ubangijinmu! Don me ba Ka aiko wani Manzo zuwa gare mu ba, har mu dinga bĩn ãyõyinKa,kuma mu kasance daga mũminai? »
48. Sa'an nan a lõkacin da gaskiya ta jẽ musu daga wurinMu, suka ce: « Don me ba a bã shi kamar abin da aka bai wa Mũsã ba? » Shin kuma ba su kãfirta ba da abin da aka bai wa Mũsã a gabãnin ( wannan ) ? suka ce: « Sihirõri biyu ne suka taimaki jũna, » kuma suka ce: « Lalle ne mũ, mãsu kãfirta ne ga dukansu? »
49. Ka ce: « To ku zo da wani littãfi daga, wurin Allah, wanda yake shi ne mafi shiryarwa daga gare su, in bĩ shi, idan kunkasance mãsu gaskiya. »
50. To, idan ba su karɓa maka ba to sai ka sani sunã bin son zuciyarsu ne kawai, kuma wãne ne mafi ɓata daga wanda ya bi son zuciyarsa, bã tãre da wata shiriya daga Allah ba? Lalle ne, Allah bã ya shiryar da mutãne azzãlumai.
( 1 ) Sanin waɗannan abũbuwa duka ga Ummiyyi a wuri mai nĩsa daga wurin da abin yaauku a ciki, da kuma nĩsa daga waɗanda abin ya fi shãfuwa, ya nũna gaskiyar abin da kake da'awa. Kuma yanã natsar da zũciyarka da zũciyar waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi hijira tãre da ku, cẽwa sunã cikin tsaron Allah.