Surah Al-'Ankabut | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 399
Suratul Al-Ankabut from 24 to 30
24. Sa'an nan bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa ( Ibrãhĩm ) fãce dai suka ce: « Ku kashe shi kõ, ku ƙõnã shi, » Sai Allah Ya tsĩrar da shi daga wutã. Lallea cikin wannan akwai ayõyi ga mutãnen da ke yin ĩmãni.
25. Kuma Ibrahĩm ya ce « Bãbu abin da kuka yi sai dai kub bar Allah kun riƙi gumãka sabõda sõyayyar tsakãninku a cikin rãyuwar dũniya, a'an nan a Rãnar Ƙiyãma sãshinku zai kãfirce wa sãshi, kuma makõmarku ita ce wutã kuma bã ku da waɗansu mataimaka. »
26. Sai Lũɗu ya yi ĩmãni da shi. Kuma Ibrãhĩm ya ce: « Lallenĩ mai ƙaura ne zuwa ga Ubangijina. Lalle Shĩ Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima. »
27. Kuma Muka bã shi Ishãƙa da Ya'aƙũba, kuma Muka sanya Annabci da littãfi a cikin zuriyarsa. Kuma Mun bã shi sakamakonsa a dũniya, kuma lalle shĩ a Lãhira, tabbas, yanã a cikin sãlihai.
28. Da Lũɗu, a lõkacin daya ce wa mutãnensa, « Lalle kũ, haƙĩƙa kunã jẽ wa alfãsha wadda wani mahalũƙi daga cikin dũniya bai riga ku gare ta ba. »
29. « Ashe, lalle kũ kunã je wa maza, kuma ku yi fashin hanya kuma ku je, a cikin majalisarku da abin da bã shi da kyau? To, jawãbin mutãnensa bai kasance ba fãce dai sun ce: 'Ka zo mana da azãbar Allah, idan ka kasance daga mãsu gaskiya.' »
30. Ya ce: « Ya Ubangijĩna! Ka taimake ni a kan mutãnen nan maɓarnata. »