Surah Al-'Ankabut | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 400
Suratul Al-Ankabut from 31 to 38
31. Kuma a lõkacin da ManzanninMu suka jẽ wa Ibrãhĩm da bushãra suka ce: « Lalle mu mãsu halaka mutãnen, wannan alƙarya ne. Lalle mutãnenta sun kasance mãsu zãlunci. »
32. Ya ce: « Lalle akwai Lũɗu a cikinta! » Suka ce: « Mũ ne mafiya sani ga waɗanda suke a cikinta, lalle munã tsĩrar da shi da mutãnensa, fãce fa mãtarsa ta kasance a cikin mãsu wanzuwa. »
33. Kuma a lõkacin da ManzanninMu suka je wa Lũɗu ya ɓãta rai sabõda su, kuma yã ƙuntata ga kirji sabõda su. Kuma suka ce: « Kada ka ji tsõro kuma kada ka yi baƙin ciki lalle mũ mãsu tsĩrar da kai ne da iyãlanka, fãce dai matarka ta kasance daga mãsu wanzuwa. »
34. « Lalle mũ, mãsu saukar da azãba ne daga sama a kan mutãnen wannan alƙarya sabõda abin da suka kasance sunã yi na fãsiƙanci. »
35. Kuma lalle Mun bar wata ãyã bayyananna daga gare ta ga mutãne mãsu hankalta.
36. Kuma zuwa ga Madyana, Mun aika ɗan'uwansu shu'aibu, sai ya ce: « Ya mutãnena! Ku bauta wa Allah kuma ku yi fatan ( rahamar ) Rãnar Lãhira, kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasã, alhãli kuwa kunã mãsu lãlãtarwa. »
37. Sai suka ƙaryata shi, sabõda haka tsãwa ta kãmã su, dõmin haka suka wãyi gari sunã guggurfãne.
38. Da Ãdawa da Samũdãwa alhãli kuwa lalle alãmun azãba sun bayyana a gare su daga gidãjensu kuma Shaiɗan ya ƙawãta musu ayyukansu, sabõda haka ya kange su daga hanyar Allah, kuma sun kasance mãsu basĩra!